Na-kusa da Turji ya fallasa asirin inda ‘Dan bindigan ke samun makamai da taimako

Na-kusa da Turji ya fallasa asirin inda ‘Dan bindigan ke samun makamai da taimako

  • Musa Kamarawa wanda na-kusa ne da Muhammad Bello wanda aka fi sani da Turji ya fasa-kai
  • A wani bidiyo, an ji Kamarawa ya bayyana sunayen masu taimakawa ta’adin gungun ‘yan bindigan
  • Wannan Bawan Allah ya fadi sirrin Turji da abokan aikinsu bayan ya ce ya yi nadamar aikinsa

Jaridar Daily Nigerian ta bayyana cewa Musa Kamarawa ya tona masu taimaka masu da bayanai da kuma masu ba su kayan sojoji, abinci da kuma kwayoyi.

Kamarawa mai shekara 33 yace a cikin gidan makaman Truji akwai bindigogi irinsu AK 47, bindiga mai lugude, abin harba roka, da na harbo jirgin sama.

A rahoton da jaridar ta fitar a ranar Asabar, 15 ga watan Junairu, 2022, Musa Kamarawa ya ce Bello Turji yana da yara birjik a duk inda ya saba kai harinsa.

Kara karanta wannan

Ta’addanci: Masu kai wa 'yan bindiga bayanai sune babbar matsalar mu, El Rufai

“Turji aboki na ne sosai, mu na magana, kuma mu na neman shawarar juna kafin mu kai hari a mafi yawan lokaci.”

- Musa Kamarawa

Masu shigo da khaki da makamai

Da yake bayani a bidiyo, wannan mutumi ya bada sunan wani Dr. Abubakar Hashimu Kamarawa a matsayin wanda yake ba ‘yan bindiga kaya da takalman sojoji.

Kamarawa wanda ‘da ne a wajen tsohon gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa ya bada sunan masu taimaka masu wajen shigo da makamai.

Na-kusa da Turji
Musa Kamarawa Hoto: www.nairaland.com
Asali: UGC

A cewar Musa Kamarawa, akwai wani ‘danuwansa Basharu da ‘yan sanda suke nema bisa zargin hada-kai da jami’an shige da fice wajen kawo makamai daga ketare.

Sauran wadanda Kamarawa ya tonawa asiri a matsayin masu hada-kai da ‘yan bindiga wajen yin ta’adi sun hada da Yahaya, Dan Tseka, Gwandi da wani Summallawa

Kara karanta wannan

Matashi da kanwarsa sun bayyana yadda tsawo da girman jikinsu ya zamo musu matsala

Masu taimakawa da miyagun kwayoyi

"Pabro yana cikinsu, wani Ibo ne da yake da shagon saida magani. Muntari Ajiya kuma bahaushe ne."

Sojoji 100 ke tsare Turji

“Turji yana da sojoji sama da 100 da suke gadin inda yake, baya ga sauran wuraren da ake tsarewa.”
“Bambancin ‘yan bindiga da sojojin ainihi shi ne kawai za a ga ‘yan bindiga gaja-gaja, yayin da sojoji suke tsaf.”

Sauran miyagu

Manyan yaran Tuji sun hada da ‘danuwansa Doso; Sani Duna, Bello Danbuzu, da su Atarwatse.

Masu turowa Bello Turji hotunan barnar da suka yi a dandalin WhatsApp su ne su Kabiru Maniya, Alhaji Shadari, a cewar wannan mutumi da yanzu ya ce ya tuba.

Inda matsalar ta ke - El-Rufai

A karshen makon nan ne Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya fito yana cewa masu ba ‘yan bindiga bayanan sirri sune manyan matsalolin da ake fama da su.

Kara karanta wannan

Shehu Sani ya yi martani kan kyautar da Tinubu ya bayar na N50n ga 'yan Zamfara

Gwamna El-Rufai ya bayyana wannan ne wajen wani jawabi da ya yi a ranar bikin tuna ‘yan mazan jiya da aka hallaka a ranar mai kamar ta jiya a shekarar 1966.

Asali: Legit.ng

Online view pixel