Juyin-mulki: Najeriya ta yi magana da babbar murya, ta gargadi Sojojin Mali su shiga taitayinsu

Juyin-mulki: Najeriya ta yi magana da babbar murya, ta gargadi Sojojin Mali su shiga taitayinsu

- Gwamnatin Najeriya ta tsoma baki kan abin da ke faruwa a kasar Mali

- Ma’aikatar harkokin waje ta fitar da wani jawabi na musamman a jiya

- Najeriya ba ta tare da sojoji a yunkurin cire shugabannin rikon kwarya

Gwamatin Najeriya ta fada wa sojojin Mali su yi maza su saki shugaban rikon kwarya na kasar Mali, Bah Ndaw da Firayim Minista, Moctar Ouane.

A wani jawabi da mai magana da yawun bakin ma’aikatar harkokin kasar wajen Najeriya, Ferdinand Nwonye, an soki tsare shugabannin da aka yi.

A ranar Talata, ma'aikatar ta fitar da wannan jawabi a shafin Twitter a madadin Najeriya.

KU KARANTA: Shugaban Libya ya ziyarci Buhari a Aso Villa

Jawabin ya ke cewa: “Gwamnatin tarayya ta na matukar tir da cigaba da tsare shugaban rikon kwarya, Bah Ndaw da Firayim Minista, Moctar Ouane.

Mista Ferdinand Nwonye ya ce: “Wannan danyen aiki abin Allah wadai ne, kuma zai dawo da hannun agogo baya wajen dawo da mulkin Farar hula a Mali.”

Ma’aikatar harkar kasar wajen ta ce matakin da sojojin suka dauka barazana ne ga zaman lafiya.

“Don haka gwamnatin tarayyar Najeriya ta na kira ayi maza a saki shugaban rikon kwaryan kasa da Firayim Minista da aka tsare ba tare da wani wata-wata ba.”

Juyin-mulki: Najeriya ta yi magana da babbar murya, ta gargadi Sojojin Mali su shiga taitayinsu
Jawabi a kan rikicin Mali Hoto: @NigeriaMFA
Asali: Twitter

KU KARANTA: Sojoji sun dauke shugaban kasar Mali da Firayim Minista Cisse

“Wadanda suke da hannu a wannan abin kunya, su sani cewa masu ruwa da tsaki a yankin da kuma aminan kasar Mali ba su goyon bayan tsare jami’ai.”

Har ila yau, jawabin ya ce gwamnatin Najeriya ba ta yarda a tursasa wa shugabannin yin ritaya ba.

Channels TV ta ce an fara rade-radin juyin-mulki a kasar Mali tun a ranar Talata, bayan da aka fahimci cewa sojoji sun kama shugabannin kasar, sun tsare su.

A shekarar bara an yi irin haka, inda Najeriya ta yi tir da abin da ya faru a Mali, bayan sojoji sun tsare shugaba Ibrahim Keita da Firayim Minista, Boubou Cisse.

A dalilin wannan juyin mulki da sojoji suka yi, shugaban kasar Mali ya yi murabus. Hakan na zuwa ne bayan tsawon lokaci ana fama da matsaloli a kasar Afrikar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel