Zamfara: 'Yan daban siyasa sun lakada wa mai sukar Matawalle duka, sun farfashe motarsa

Zamfara: 'Yan daban siyasa sun lakada wa mai sukar Matawalle duka, sun farfashe motarsa

  • Wasu miyagu da ake zargin 'yan daban siyasa ne sun yi wa Shamsu Kasida, babban mai sukar Gwamna Matawalle, dukan kawo wuka
  • 'Yan daban sun bayyana da miyagun makamai inda suka yi wa Kasida duka tare da farfashe masa gilasan mota a wani gidan cin abinci a Gusau
  • Da kyar jama'ar da ke wurin suka kwace Kasida inda daga nan aka garzaya da shi wani asibiti, an kwantar da shi rai a hannun Allah
  • Maharan sun hanzarta shigewa gidan gwamnatin jihar bayan dukan Kasida, matashi mai goyon bayan Sanata Kabir Marafa, abokin adawar Matawalle

Zamfara - Makonni biyu bayan kai farmaki ofishin wata jaridar yanar gizo da gidan talabijin, wasu da ake zargin 'yan daban siyasa ne a ranar Juma'a sun kai mummunan farmaki kan mai sukar Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara inda suka ragargaza motarsa a Gusau.

Kara karanta wannan

Katsina: Masari ya yi umarnin bude dukkan gidajen mai da kasuwannin shanu a jihar

An lakada wa Shamsu Kasida mugun duka kuma an farfasa motarsa yayin da ya tsaya a wani wurin cin abinci da ke kusa da gidan gwamnatin jihar a Gusau, Premium Times ta ruwaito.

Manajan daraktan gidan talabijin na Thunder Blowers, Anas Anka, ya zargi gwamnan jihar da daukar nauyin farmakin farko. Ya ce a tuhumi gwamnan a duk lokacin da mummunan lamari ya faru da shi ko ma'aikacinsa.

Zamfara: 'Yan daban siyasa sun lakada wa mai sukar Matawalle duka, sun farfashe motarsa
Zamfara: 'Yan daban siyasa sun lakada wa mai sukar Matawalle duka, sun farfashe motarsa. Hoto daga premiumtimesng.com
Asali: UGC

Wanda aka kai wa farmakin mai suna Shamsu Kasida, gagarumin mai sukar gwamnan ne a kafafen sada zumunta. Ya na goyon bayan Sanata Kabir Marafa, daya daga cikin abokan adawar Matawalle.

Daga Marafa har Matawalle 'yan jam'iyyar All Progressives Congress (APC), amma Marafa ya na sukar yadda aka mayar da shi da Abdulaziz Yari gefe a hedkwatar jam'iyyar mai mulki.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda suna neman wuce gona da iri a jihohin mu, Zulum da Matawalle sun koka

Wani abokin Kasida, wanda ya zanta da Premium Times a waya, Ismaila Salmanu, ya zargi cewa 'yan siyasa ne suka dauka nauyin harin.

"Kasida ya na tsaye a wani gidan cin abinci mai suna Yandoto yayin da 'yan daba suka fara dukansa. Suna dauke da miyagun makamai. Yayin da suke dukansa, daya daga cikinsu ya yi amfani da adda," yace.

Gidan cin abinci na Yandoto fitacce wuri ne a Gusau kuma mallakin Marafa ne sannan ya na titi daya da gidan gwamnatin jihar. Gidan cin abincin kai tsaye ya ka kallon gidan gwamnatin.

Salmanu ya ce 'yan daban sun tsaya da dukan Kasida ne bayan wasu mutane da ke wurin sun shiga. Amma kuma, 'yan daban sun farfashe gilasan motarsa kirar Honda Accord.

"Wasu daga cikin abokanmu da ke tare da Kasida yayin farmakin sun ce 'yan daban sun tsere zuwa cikin gidan gwamnatin bayan farmakin. Mun kai shi wani asibiti mai zaman kansa inda aka bashi gado. Ya samu miyagun raunika amma ba zan iya aiko da hotunansa yanzu ba," Salmanu yace.

Kara karanta wannan

Ana sakin 'yan bindiga ba tare da hukunci ba, Gwamna Matawalle ya koka

Wata majiya wacce ta bukaci a boye sunan ta, ta ce 'yan ta'addan sun samu jagorancin gagarumin shugaban 'yan daban Gusau, Danda Jan Wuya.

Mai magana da yawun Matawalle, Zailani Bappa, ya ki amsa kiran da aka yi masa kan lamarin amma ya ce gwamnatin jihar ba za ta martani kan zargin mutanen da ke neman suna ba.

Ana sakin 'yan bindiga ba tare da hukunci ba, Gwamna Matawalle ya koka

A wani labari na daban, Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya ce daga cikin dalilan da suke assasa wutar ta'addanci akwai kyale 'yan bindigar da 'yan ta'adda da ake yi babu wani hukunci.

A cewar gwamnan, sau da yawa ana sakin 'yan bindigan daji ba tare da an yi musu wani hukunci ba, Daily Trust ta ruwaito.

Matawalle ya sanar da hakan ne a ranar Laraba yayin da ya karba wakilan gwamnatin tarayya yayin da suka je masa ziyarar jaje kan hare-haren da aka kai wa wasu yankunan kananan hukumomin Anka da Bukkuyum a jihar.

Kara karanta wannan

Kaduna: Iyaye da malamai sun yi martani kan aikin kwana 4 na makarantun gwamnati

Asali: Legit.ng

Online view pixel