Yan Najeriya su rika yi mana adalci kan lamarin tsaro, muna kokari: Shugaba Buhari

Yan Najeriya su rika yi mana adalci kan lamarin tsaro, muna kokari: Shugaba Buhari

  • Shugaba Buhari ya karbi bakuncin tawagar shugabannin darikar Tijjaniya ranar Juma'a a Abuja
  • Gwamnan Ganduje ya kai manyan Malaman Najerya don gudanar da addu'o'i neman zaman lafiya
  • Shugaba Buhari ya bayyana cewa Najeriya tafi tsaro yanzu fiye da lokacin da ya karbi mulki a 2015

FCT, Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa gwamnatinsa ta yi iyakan kokarinta wajen magance ta'addanci amma ba za suyi kasa a gwiwa ba.

Hakazalika ya yi kira ga yan Najeriya su yiwa gwamnatinsa adalci idan suna magana kan lamarin tsaro dubi ga yadda ya samu kasar a 2015 lokacin da ya hau mulki.

A cewarsa, Gwamnatinsa ta samu nasarori da dama musamman a yankin Arewa maso gabas da Kudu maso kudancin Najeriya.

Kara karanta wannan

Hotunan Buhari yayin da ya ziyarci iyalan Marigayi Shonekan don yi masu ta’aziyya

Mun yi iyakan kokarinmu kan matsalar tsaro, Shugaba Buhari
Mun yi iyakan kokarinmu kan matsalar tsaro, Shugaba Buhari Hoto: Presidency
Asali: Facebook

Buhari ya bayyana hakan ne ranar Juma'a yayinda ya karbi bakuncin Shugaban darikar Tijjaniyya na duniya, Tidjani Ali Bin Arabi, a fadar Aso Villa, Abuja.

Yace:

"Mun yi iyakan kokarinmu, kuma zamu cigaba da aiki da tsare-tsaren yaki da ta'addanci. Ina kyautata zato Allah ya amsa addu'o'inmu."

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, wanda ya kai Malamin wajen Buhari ya bayyana cewa sun gayyaceshi Najeriya ne domin addu'a bisa matsalolin tsaron da kasar ke ciki.

Wadanda suka halarci zaman sun hada da Mai martab a Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero; Sheikh Dahiru Usman Bauch; Ministan Sadarwa, Dr Isa Ali Pantami, dss.

'Yan Boko Haram sun sace malaman makarantar 'yan sanda a Borno

A wani labarin kuwa, yan ta’addan Boko Haram sun sace wasu ‘yan sandan mobal da ba a tantance adadinsu ba a makarantar horar dasu da ke karamar hukumar Gwoza a jihar Borno, mahaifar Sanata Ali Ndume, shugaban kwamitin majalisar dattawa kan sojoji.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Tsohon gwamna, kuma jigon jama'iyyar APC ya riga mu gidan gaskiya

Bayanin da jaridar Punch ta samu ya nuna cewa ‘yan ta’addan sun kai hari makarantar horon ne da misalin karfe 8:22 na ranar Alhamis 13 ga watan Janairu da daddare.

Asali: Legit.ng

Online view pixel