Addini, rashin lafiya, da matsaloli 7 da Tinubu zai fuskanta a wajen neman Shugaban Najeriya

Addini, rashin lafiya, da matsaloli 7 da Tinubu zai fuskanta a wajen neman Shugaban Najeriya

  • A farkon makon nan ne Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar da cewa zai yi takara a zaben 2023
  • Shakka babu, Bola Ahmed Tinubu yana cikin manyan ‘yan siyasan da ake ji da su a fadin kasar nan
  • Sai dai tsohon gwamnan na jihar Legas ya na fuskantar wasu barazana wajen cinma dadadden burinsa

Legit.ng Hausa ta tattaro jerin wasu abubuwa da ake ganin za su kawowa Bola Ahmed Tinubu cikas a siyasa yayin da ya kwallafa ransa a fadar Aso Villa.

1. Abokin takara

Asiwaju Bola Ahmed Tinubu Musulmi ne, don haka ake sa ran zai dauko kirista a matsayin mataimakinsa idan zai yi takara, to sai dai, nan kuma fa daya.

Idan Bola Tinubu ya dauko kirista, da wuya ya samu karbuwa a Arewacin Najeriya. Idan ya zabi ya yi takara da Musulmin Arewa, zai sha kasa yankin Kudu.

2. Rashin lafiya

A wani rahoto da BBC Hausa ta fitar, rashin isasshen lafiya shi ne babban kalubalen da Tinubu zai fuskanta. Kusan akwai shakku game da lafiyarsa da shekarunsa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da bai da lafiya kwanaki, shugaba Muhammadu Buhari da kansa, ya je ya duba shi a Landan.

3. Alamar tambaya a kan dukiya

Ana zargin cewa Bola Ahmed Tinubu yana da tarin dukiya. Tambayar da za ayi tayi idan ya tsaya takara a zaben 2023 shi ne ina ya samu irin wannan kudin haka?

4. Ina takardunsa?

Baya ga alamar tambaya a kan dukiya da shekarunsa, akwai tantama a game da karatun Tinubu. Akwai zargin ma bai yi karatu a Government College Ibadan ba.

Kamfe
Tinubu da 'Yan APC a kamfe Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

Har yau ana ce-ce-ku-ce kan gaskiyar inda ‘dan siyasar ya yi digiri. Daga University of Chicago, sai wata rana a ce ai Richard Daley Community College ya je.

5. Kifin rijiya?

A wani rubutu da aka yi a Daily Trust, an ce duk da Tinubu ya zama jigon siyasar Yarbawa, zai yi masa wahala ya samu kuri’a a Kudu maso gabas da Neja Delta.

Rahotanni sun nuna ‘Yan Arewa ba za su goyi bayansa ba saboda zargin abin da ya faru a zaben Kano a 2019 da barnar da ‘Yan OPC suka yi da yana gwamna.

6. Sauran manyan APC

Duk da cewa da gumin irinsu Bola Tinubu aka kafa jam’iyyar APC a 2013, sai dai zai iya gamuwa da cikas a 2023 daga wasu ‘yan jam’iyyarsa da suke da buri iri daya.

7. Gwamnatin Buhari

Jagoran na APC zai so ya zama magajin Muhammadu Buhari, amma akwai mutane da yawa da suke ganin babu abin kirkin da gwamnatin APC ta tabuka a kasa.

Makarkashiya a APC

Dazu kun ji ana zargin kwamitin Gwamna Mai Mala Buni bai da niyyar shirya zaben shugabannin jam’iyyar APC na kasa domin a karya irinsu Tinubu.

Buni ya kuma samu goyon bayan wasu Gwamnonin APC da Ministan shari’a, Abubakar Malami SAN, har ya shantake ya fara hangen mataimakin shugaban kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel