Rudani: 'Yan Boko Haram sun sace malaman makarantar 'yan sanda a Borno

Rudani: 'Yan Boko Haram sun sace malaman makarantar 'yan sanda a Borno

  • 'Yan Boko Haram sun kai mummunan hari jihar Borno, sun sace wasu malaman makarantar horar da 'yan sanda
  • Lamarin ya faru ne a jiya Alhamis 13 ga watan Janairu, inda suka yi harbe-harbe kafin su gudu
  • Harin na 'yan ta'addan Boko Haram ya biyo bayan wata ziyarar aiki da kwamitin majalisar dattijai kan sojoji ta kai yankin

Borno - ‘Yan ta’addan Boko Haram sun sace wasu ‘yan sandan mobal da ba a tantance adadinsu ba a makarantar horar dasu da ke karamar hukumar Gwoza a jihar Borno, mahaifar Sanata Ali Ndume, shugaban kwamitin majalisar dattawa kan sojoji.

Bayanin da jaridar Punch ta samu ya nuna cewa ‘yan ta’addan sun kai hari makarantar horon ne da misalin karfe 8:22 na ranar Alhamis 13 ga watan Janairu da daddare.

Kara karanta wannan

Kano ce jiha mafi zaman lafiya a Najeriya: Jerin adadin mutanen da aka kashe a 2021

'Yan Boko Haram sun kai hari Borno
Da dumi-dumi: 'Yan Boko Haram sun sace malaman makarantar 'yan sanda a Borno | channelstv.com
Asali: UGC

An ce sun zo da manyan motocin bindiga ne, inda suka yi ta harbe-harben iska kafin su yi awon gaba da malaman ‘yan sandan na mobal.

Makarantar horarwar tana da nisan kilomita ashirin da biyar daga garin Gwoza.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gwoza gari ne mai iyaka tsakanin Borno da karamar hukumar Madagali ta jihar Adamawa.

Kwamitin majalisar dattijai kan sojoji karkashin jagorancin Sanata Ali Ndume ya kai ziyarar aiki zuwa rundunar ‘yan wasan Operation Hadin Kai, a yankin kwanaki biyu da suka gabata.

Ba a sace dan sanda ko daya ba

A bangare guda, kwamishinan ‘yan sandan jihar Borno, Abdul Umar, ya ce babu wani jami’in ‘yan sandan mobal da ‘yan Boko Haram suka sace a harin, Vanguard ta rahoto.

Hakazalika, ya kara da cewa an kai hari a kwalejin, amma ‘yan sanda sun yi nasarar fatattakar maharan.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Yan bindiga sun kai hari Plateau Poly, sun kwashe dalibai

Umar, yayin da yake magana da manema labarai a Maiduguri a ranar Juma’a, ya bayyana rahoton da aka buga a matsayin mara tushe, yana mai cewa:

“An jawo hankalin rundunar ‘yan sandan jihar Borno kan labaran da ake yadawa a shafukan sada zumunta, inda suka yi zargin cewa wasu jami’an PMF da ba a bayyana adadinsu ba an yi garkuwa da su a kwalejin horar da ‘yan sanda ta mobal da ke Gwoza."

A wani labari, Farfesa Umara Babagana Zulum, Gwamnan jihar Borno ya ce mayakan ta'addanci ISWAP sun fi na Boko Haram miyagun makamai, don haka dole a dakile su da gaggawa.

Gwamnan ya yi jawabin ne yayin da ya tarbi mambobin kwamitin majalisar dattawa na kula da harkokin sojoji karkashin jagorancin Ali Ndume. Shugabannin sun ziyarci Zulum a Maiduguri, babban birnin jihar Borno, TheCable ta ruwaito.

Yayin jinjina ga gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da hukumomin tsaro na tarin nasarorin da suka samu a Borno, Zulum ya bayyana tsananin damuwarsa da karuwar yawan mayakan ISWAP a sassan jihar, musamman a kudancin Borno.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: 'Yan bindiga sun sace fasinjoji a Imo yayin da suka hanyar zuwa Legas

Asali: Legit.ng

Online view pixel