Sanata Ndume ya karyata harin Boko Haram kan cibiyar horar da yan sanda a Gwoza

Sanata Ndume ya karyata harin Boko Haram kan cibiyar horar da yan sanda a Gwoza

  • Sanata Ali Ndume ya yi martani a kan rahotannin cewa mayakan Boko Haram sun kai farmaki kauyen Limankara da ke jihar Borno tare da sace yan sanda
  • Ndume ya ce karya ne babu wani abu makamancin haka da ya wakana a yankin na karamar hukumar Gwoza
  • Ya ce a yanzu haka akwai zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin, sannan ya ce akwai rundunar soji girke wadanda ke ragargazan mayakan da ke fitowa daga dajin Sambisa

Borno - Sanata Mohammed Ali Ndume ya yi martani a kan rahotannin da ke cewa mayakan Boko Haram sun sace jami'an yan sanda a farmakin da suka kai kauyen Limankara da wasu yankunan karamar hukumar Gwoza na jihar Borno.

Ndume wanda ya fito daga yankin Gwoza kuma yake wakiltan yankin Borno ta kudu a majalisar dattawa ya karyata batun ne a yayin wata hira da jaridar Vanguard a Maiduguri, a ranar Juma'a, 14 ga watan Janairu.

Kara karanta wannan

Kwastam ta kama litar man fetur 30,150 daga hannun masu fasakwabri zuwa kasar waje

Sanata Ndume ya karyata harin Boko Haram kan cibiyar horar da yan sanda a Gwoza
Sanata Ndume ya karyata harin Boko Haram kan cibiyar horar da yan sanda a Gwoza Hoto: Vanguard
Asali: Twitter

Ya bayyana cewa akwai zaman lafiya da kwanciyar hankali a garin Limankara da sauran kauyukan da ke kewaye, inda yace an girke rundunar tsaro a wurare masu muhimmanci.

Ya kuma ce bataliyan na ta ragargazan mayakan Boko Haram da ke ketarowa daga dajin Sambisa zuwa tsaunukan Mandara da ke yankin Kamaru a kullun.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ndume ya ce:

"Ba gaskiya bane cewa an yi garkuwa da wasu jami'an yan sanda a Limankara, a zahirin gaskiya ma, babu jami'an yan sanda a Limankara, bataliyan rundunar soji ne kadai muke da shi a Limankara wadanda ke aiki ba kakkautawa, kuma babu wani hari makamancin haka."

'Yan Boko Haram sun sace malaman makarantar 'yan sanda a Borno

A baya mun ji cewa ‘Yan ta’addan Boko Haram sun sace wasu ‘yan sandan mobal da ba a tantance adadinsu ba a makarantar horar dasu da ke karamar hukumar Gwoza a jihar Borno, mahaifar Sanata Ali Ndume, shugaban kwamitin majalisar dattawa kan sojoji.

Kara karanta wannan

Kashe-kashen Filato: Kada wata kungiya ta dauki doka a hannunta, in ji Buhari

Bayanin da jaridar Punch ta samu ya nuna cewa ‘yan ta’addan sun kai hari makarantar horon ne da misalin karfe 8:22 na ranar Alhamis 13 ga watan Janairu da daddare.

An ce sun zo da manyan motocin bindiga ne, inda suka yi ta harbe-harben iska kafin su yi awon gaba da malaman ‘yan sandan na mobal.

Asali: Legit.ng

Online view pixel