Nasara daga Allah: Sojoji sun yi kaca-kaca da kasuwar 'yan Boko Haram/ISWAP

Nasara daga Allah: Sojoji sun yi kaca-kaca da kasuwar 'yan Boko Haram/ISWAP

  • Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da yin kaca-kaca da wata kasuwar 'yan Boko Haram a wani yankin jihar Borno
  • Wannan lamari ya kai ga hallaka wasu 'yan ta'adda uku tare da fatattakar wasu daga cikinsu a yayin harin
  • Hakazalika, an kwato bindiga da sauran makamai daga hannun 'yan ta'addan, kamar yadda rahotanni suka tabbatar

Borno - Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarun Operation Hadin Kai sun kashe ‘yan ta’adda akalla uku a wani samame da suka kai a Damask ta jihar Borno.

Har ila yau, ta ce sojojin sun lalata wata haramtacciyar kasuwa da ‘yan ta’addan ke gudanar da hada-hadarsu, kamar yadda jaridar Punch ta rahoto.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Daraktan hulda da jama’a na rundunar, Onyema Nwachukwu, ya fitar ranar Asabar a Abuja.

Kara karanta wannan

Ku bayyana maboyar 'yan bindiga, Babban limamin Masallacin kasa ga 'yan Najeriya

Yadda aka hallaka 'yan Boko Haram da kone kasuwarsu
Nasara daga Allah: Sojoji sun yi kaca-kaca da kasuwar 'yan Boko Haram | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Nwachukwu, Birgediya-Janar, ya ce sojojin na 5 Brigade, Sector 3 a lokacin da suke kara kaimi wajen tunkarar ‘yan ta’addan sun samu gagarumar nasara a kan ‘yan ta’addan a ranar Juma’a.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kara da cewa, rundunar sojojin, a yayin da suke gudanar da aikin share fage mai suna “Operation Dominance I,” sun yi arangama da ‘yan ta’addan a wata haramtacciyar kasuwa da ‘yan ta’addan ke hada-hadarsu a kauyen Gallo Malawari.

Hakazalika, ya bayyana yadda wasu daga cikin 'yan ta'adda suka tsere yayin da rundunar sojin ta yi ruwan wuta kan 'yan ta'addan.

Daily Nigerian ta tattaro Nwachuku na cewa:

“Sojoji sun kwato bindiga kirar AK 47 daya, babbar mota, babura biyu, mujallun alburusai guda hudu da babu komai a ciki da harsashi 7.62mm da dai sauransu.”

An kashe 'yan Boko Haram 950, 24,059 sun mika wuya a kasa da watanni 7

Kara karanta wannan

Innalillahi: 'Yan bindiga sun dasa bama-bamai a ofishin 'yan sanda, sun saki masu laifi

A wani labarin, dakarun Operation Hadin Kai, sun kawar da ‘yan ta’addan Boko Haram/ISWAP 950 a yankin Arewa maso Gabas tsakanin 20 ga Mayu, 2021 zuwa 6 ga Janairu, 2022, kamar yadda hedkwatar tsaro ta bayyana, Daily Nigerian ta rahoto.

Mukaddashin Daraktan Ayyukan Yada Labarai na Tsaro, Maj.-Gen. Bernard Onyeuko ne ya bayyana haka a lokacin da yake bitar yadda ayyukan suke gudana a ranar Alhamis a Abuja.

Mista Onyeuko ya ce sojojin sun kawar da wasu manyan kwamandoji da kuma shugabannin kungiyoyin ta’addanci a lokacin.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel