Bidiyon katafaren gida da miloniya ta mutu ta bar shi babu magaji, har da motar zinare

Bidiyon katafaren gida da miloniya ta mutu ta bar shi babu magaji, har da motar zinare

  • Wani bidiyo ya nuna yadda wani katafaren gida wanda cikinsa akwai motar zinare su ka lalace bayan mutuwar mai gidan
  • Kasaitaccen gidan ya zama kango a halin yanzu saboda babu waɗanda su ke kulawa da su duk da kuwa na miliyoyi ne
  • Mutane da dama sun bayyana ra'ayoyin su dangane da rashin dacewa a kan yadda aka bar gidan ba tare da sanya wani wanda zai kula da tarin dukiyar ba

Wani matashi mai suna Steve Ronin ya wallafa bidiyon gidan wata attajira wacce ta gina gida tun shekarun 1950s. Babu kowa a cikin gidan tun bayan mutuwar matar a shekarar 2000.

Yayin da Ronin ya ke zagayawa cikin gidan, ya faɗa cewa gidan sauƙaƙaƙƙe ne wanda ba a cika masa ƙawa ba. Ɗaya daga cikin abokan aikin sa ya bugi bangon gidan inda su ka lura da motsin wani abu.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Saurayi ya kashe mahaifin budurwarsa ta hanyar daɓa masa wuƙa yayin da ya kama su suna tsakar 'soyewa' a gidansa

Bidiyon katafaren gida da miloniya ta mutu ta bar shi babu magaji, har da motar zinare
Bidiyon katafaren gida da miloniya ta mutu ta bar shi babu magaji, har da motar zinare. Hoto daga Steve Ronin
Asali: Facebook

An ajiye mata wasiƙa

Da akai duba zuwa wajen ɗakin kwana, an nuna kayan ɗakin a hargitse. Mutumin ya ce wurin ya nuna alamun samun baƙi kwanan nan, ta iya yiwuwa wani mai daukar hoto.

Motsin da su ka ji da farko an gano cewa na wata dabba ce. Akwai wani ɗan ƙaramin gado na mutum ɗaya a cikin gidan da kuma wata wasiƙa da ke tambayar yadda marigayiyar ta ke.

A lokacin rubuta wannan rahoton, sama da mutane miliyan 3 su ka kalli bidiyon, sannan sama da mutane dubu sun nuna yadda bidiyon ya birge su.

Jama'a sun yi martani

Legit.ng ta tattaro mu ku ƙadan daga ra'ayoyin da mutane su ka bayyana karkashin bidiyon.

Brian Mclntyre ya ce:

Kara karanta wannan

Duniya ba tabbas: Bidiyon motar alfarma da gida da wata miloniya ta mutu ta bari babu magada, har sunyi tsatsa

“Kamar wanda ya ke daukar bidiyon ya zamiye kasa. A sake wani lalen.”

Marty Byrde ya ce:

“A wacce duniya aka taba wannan miloniyar.”

Peya Salvacion ta ce:

“Ita kadai aka bar ta, babu mai kulawa da tsohuwar? Gaskiya duk na ji babu dadi... Aka kuma bar duk wadannan kayan alatun.. babu wanda ya ci gaba da kulawa da gidan?

Ina fatan ninka yawan 'ya'ya na, Magidanci mai yara 9 da ke cikin tsananin talauci da rashi

A wani labari na daban, wani magidanci dan asalin kasar Zimbabwe ma 'ya'ya 9 wanda ke zaune a daki ciki da falo, cike da abin mamaki ya bayyana burinsa na ninka yawan yaran da ya mallaka.

Ernest Chinuwo, ya na zaune tare da iyalinsa a wani ragargajajjen bukka kuma a wani kwari mai ruma a wajen garin Usanga a Chipinge, shafin Linda Ikeji ya ruwaito.

Kafar watsa labaran kasa ZBC ta ruwaito yadda mutumin ya ce ya na zama a kwarin, bayan wani ya sa shi ya zama mai kula da gurin. Mai gurin ya na zaune a kasar Afirika ta kudu.

Kara karanta wannan

Duniya kenan: Yadda aka kama wani mutum da ke cin hanjin 'yan adam a Zamfara

Asali: Legit.ng

Online view pixel