Duniya ba tabbas: Bidiyon motar alfarma da gida da wata miloniya ta mutu ta bari babu magada, har sunyi tsatsa

Duniya ba tabbas: Bidiyon motar alfarma da gida da wata miloniya ta mutu ta bari babu magada, har sunyi tsatsa

  • Wani bidiyo ya nuna wani gida da aka banzatar da mota kirar Mustang a ciki bayan mutuwar mai gidan
  • Kyakyyawan gidan ya fita a hayyacinsa sakamakon rashin masu kula dashi da dukiyar da ke ciki
  • Da yawa daga cikin wanda suka yi magana, sun bayyana illar rashin iyali da za su kula da dukiya idan mutum ya rasu

Wani matashi, Steve Ronin, ya wallafa bidiyon wani katafaren gida da aka gina a shekarun 1950s. An banzatar da gidan bayan rasuwar mai gidan a shekara ta 2000.

Duniya ba tabbas: Bidiyon motar gwal da gida da wata miloniya ta mutu ta bari suna tsatsa, mutane sun magantu
Motar gwal da gida da wata miloniya ta mutu ta bari sunyi tsatsa, mutane sun magantu. Hoto: Steve Ronin
Asali: Facebook

Da yake zagayawa a gidan, Steve ya bayyana cewa gidan ba shi da fasali ko tsarin wahalan yi. Daya daga cikin 'yan tawagarsa ya daki bangon gidan kuma sunji motsi.

Kara karanta wannan

Duniya kenan: Yadda aka kama wani mutum da ke cin hanjin 'yan adam a Zamfara

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ta bar wasika

Hoton cikin falon ya nuna wasu tsofaffin kujeru da kayan daki. Mutumin ya ce kamar an samu baƙi sun kai ziyara kwanan nan, watakila masu ɗaukar hoto.

Daga baya an gano cewa motsin da aka ji ashe dabba ne. An gano wani karamin gado a cikin gidan da wasika da aka rubuta ana tambayar mai gidan ko yaya jikinta.

Kalli bidiyon a kasa:

Zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, sama da mutum miliyan uku ne suka kalli bidiyon tare da dubban masu dangwala like.

Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin sharhin mutane;

Brian Mclntyre ya ce:

"Duh, kace masu daukar hoto sun cika wajen"

Lisa Acker ya ce:

"Kada ka sauya ziyarar da ka fara kai wa da farko zuwa shirme na neman kwankwamai."

Kara karanta wannan

Hotunan yadda ginin wurin Ibada ya hallaka mutane suna tsaka da bautar Allah

Marty Bryde cewa ya yi:

"A wace duniyar ne irin wannan suke zama masu kudi, abin dariya."

Peya Salvacion ya ce:

"Ita kadai babu wanda ya kula da dattijuwar? Abin ya fara bata min rai ... kuma ta rasu ta bar dukkan wannan dukiyar ... babu wanda ya taba kulawa da gidan?"

Tsoho mai shekaru 84 da ya bar gida tsawon shekaru 47 ya dawo, ya nuna ɓacin ransa don matansa 2 sun sake aure

A wani labarin daban, wani tsoho mai shekaru 84, Peter Oyuk ya sha mamakin yadda matan sa 2 suka sake aure bayan ya yi tafiya tsawon shekaru 47.

Kamar yadda LIB ta ruwaito daga The Standard, mutumin ya bar kauyen Makale dake Malava bangaren Kakamega a shekarar 1974 lokacin yana da shekaru 37.

Ya sanar da iyalan sa cewa ya tafi neman arziki don tallafa wa matan sa 2 da yaran sa 5 duk da dai bai sanar da su lokacin da zai dawo ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel