Zamu kammalawa yankin Yarbawa manyan tituna biyu a shekarar nan, Shugaba Buhari

Zamu kammalawa yankin Yarbawa manyan tituna biyu a shekarar nan, Shugaba Buhari

  • Bayan kaddamar da manyan tituna uku a Ogun, Shugaba Buhari yayi alkawarin gwamnatinsa zata kammala wasu ayyuka biyu
  • Shugaba Buhari ya kai ziyarar kaddamar da ayyuka bisa gayyatar Gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun
  • Shugaban kasan ya jinjinawa Gwamnan inda yace lallai ya wakilci jam'iyyar APC yadda ya kamata

Shugaba Muhammadu Buhari ya tabbatarwa yan Najeriya cewa za'a kammala manyan tituna biyu da ake kan ginawa a yankin kudu maso yamma kafin karshen shekarar 2022.

Manyan titunan sune Sagamu-Benin da Legas-Ibadan.

Femi Adesina, mai magana da yawun Shugaban kasa, yace Buhari ya bada wannan tabbaci ne lokacin da ya kaddamar da manyan ayyuka biyar a jihar Ogun ranar Alhamis.

Manyan ayyukan sune:

1. Gateway City Gate

2. Babban titin Sagami-Abekuta mai tsayin kilomita 42

Kara karanta wannan

An rangaɗa wa shugaba Muhammadu Buhari sabbin sunaye biyu a jihar Ogun

3. Titin Ijebu-Ode-Epe mai tsayin 14km

4. Rukunin gidaje a Kobape

5. Rukunin gidaje a Oke-Mosan

Zamu kammalawa yankin Yarbawa manyan tituna biyu a shekarar nan, Shugaba Buhari
Zamu kammalawa yankin Yarbawa manyan tituna biyu a shekarar nan, Shugaba Buhari
Asali: Facebook

An rangaɗa wa shugaba Muhammadu Buhari sabbin sunaye biyu a jihar Ogun

Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya samu sabbin sunaye biyu a jihar Ogun yayin da ya kai ziyara domin kaddamar da ayyuka 5 da Gwamna Dapo Abiodun, ya kammala.

PM News ta rahoto cewa an rangaɗa wa shugaba Buhari sunan, 'Omowale'.

Da yake tabbatar da sabon sunan shugaba Buhari, gwamna Dapo Abiodun, ya sake rangaɗa wa Buhari alamar 'Ƙusan jihar Ogun,' kuma ya bayyana shi a matsayin ɗan jihar Ogun.

Asali: Legit.ng

Online view pixel