An rangaɗa wa shugaba Muhammadu Buhari sabbin sunaye biyu a jihar Ogun

An rangaɗa wa shugaba Muhammadu Buhari sabbin sunaye biyu a jihar Ogun

  • A yau ne shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya fara ziyarar aiki ta kwana ɗaya a jihar Ogun dake kudu maso yammacin ƙasar nan
  • Yayin wannan ziyara shugaba Buhari, wanda ya fara aikin soja a Abeokuta, ya samu sabbin sunaye biyu da aka raɗa masa
  • Buhari ya nuna farin cikinsa kan yadda gwamna Dapo Abiodun ke gwangwaje al'ummar jihar Ogun da ayyukan raya ƙasa

Ogun - A ranar Alhamis, shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya samu sabbin sunaye biyu a jihar Ogun yayin da ya kai ziyara domin kaddamar da ayyuka 5 da Gwamna Dapo Abiodun, ya kammala.

PM News ta rahoto cewa an rangaɗa wa shugaba Buhari sunan, 'Omowale' yayin da ya yi alƙawarin kammala manyan ayyuka biyu da suka shafi jihar a wannan shekarar.

Kara karanta wannan

Zamu kammalawa yankin Yarbawa manyan tituna biyu a shekarar nan, Shugaba Buhari

Da yake tabbatar da sabon sunan shugaba Buhari, gwamna Dapo Abiodun, ya sake rangaɗa wa Buhari alamar 'Ƙusan jihar Ogun,' kuma ya bayyana shi a matsayin ɗan jihar Ogun.

shugaba Buhari da gwamna Dapo Abiodun
An rangaɗa wa shugaba Muhammadu Buhari sabbin sunaye biyu a jihar Ogun Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

Shin Buhari yana da alaƙa da Ogun?

Shugaba Buhari ya fara aikin sojan shi a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun, bayan kammala makarantar horar da sojoji dake Aldershot, ƙasar Ingila.

Buhari na da shekara 20 a duniya ya zama lieutenant a gidan soja kuma aka naɗa shi kwamandan Bataliyar sojojin ƙasa dake Abeokuta.

Jawabin shugaban Buhari a Ogun

Da yake jawabi ga dandanzon mutanen jihar Ogun, shugaba Buhari ya yaba wa gwamna Dapo Abiodun, bisa dumbin ayyukan raya ƙasa da yake wa al'ummarsa, duk da ƙalubalen da ake fama da shi na annobar korona.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Shugaba Muhammadu Buhari ya dira jihar Ogun, ya fara kaddamar da ayyuka

Shugaban ya kira gwamnan da, "Gwamna mai aiki tukuru," kuma yace ayyukan da gwamnan ke yi su ne misali lamba ɗaya na, "kyaun alƙawari cikawa."

Buhari yace

"Wannan yasa jihar Ogun ta zama ɗaya daga cikin jihohin da babu tashin-tashina kuma take zaune lafiya, kuma nan ne muradin masu son zuba hannun jari."
"Kana (Dapo Abiodun) wakiltar jam'iyyar mu ta APC yadda ya kamata a jihar Ogun, kuma ka wajabta wa kanka yin aiki ga mutanen dake karkashinka."

A wani labarin kuma Tsohon gwamnan Zamfara ya sanar da kudirin takarar shugaban ƙasaba 2023, ya samu gagarumin goyon baya

Wata kungiya ta sadaukar da kanta wajen yaɗa manufar takarar shugaban ƙasa na tsohon gwamnan Zamfara, Sani Yerima.

Kungiyar karkashin Yerima Support Organisation (YSO), ta raba wa mambobinta wayoyi da motoci domin fara yakin neman zabe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel