Saboda tsabar gudu, Direban tirela ya kashe yara biyu a gaban shagon mahaifiyarsu

Saboda tsabar gudu, Direban tirela ya kashe yara biyu a gaban shagon mahaifiyarsu

  • Jama'a sun kusa hallaka wani direba da ya buge yara yan makaranta hudu a bakin shagon mahaifiyarsu
  • Mutum biyu cikin yaran sun tsallake rijiya da baya yayinda guda biyu suka rigamu gidan gaskiya
  • Jami'an yan sanda sun damke direban kuma an gurfanar da shi gaban kotun majistare

Remo - Direban Tirela, Moshood Gbadamosi, ya hallaka yara biyu, Olamide Opeyemi da Damilola Opeyemi a garin Ilisan-Remo dake jihar Ogun ranar Juma'ar da ta gabata.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa wannan mumunan hadari ya auku ne gaban shagon mahaifiyarsu.

Wata makwabciya, Olayinka Oremuyiwa, ta bayyanawa manema labarai cewa yara hudu Direban ya buge yayinda suke tsaye bakin titi.

Tace an garzaya da su asibitin koyarwan jami'ar Babcock kafin suka mutu.

Tace:

"Mutum biyu cikinsu sun rayu, amma yaronta na biyu wanda zai cika shekaru 15 a Maris da dan autan sun mutu."

Kara karanta wannan

‘Yan bindiga sun sace wani shugaban kwastam mai ritaya a gonarsa a Kwara

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Da na isa wajen, na ga mutane sun taru. Na ga mahaifiyarsu Abosede tare da Olamide (daya daga cikin yaran da aka buge). Mun yi kokarin tsayar da motoci mu kaita asibiti, amma sun ki tsayawa."
"Daga karshe kan babur muka kai yarinyar asibiti. A lokacin na samu labarin tuni an kai karamar, Damilola asibiti."

Direban tirela ya kashe yara biyu a gaban shagon mahaifiyarsu
Saboda tsabar gudu, Direban tirela ya kashe yara biyu a gaban shagon mahaifiyarsu Hoto: Punch Metro
Asali: UGC

An yiwa direban ribiti

Wani mai idon shaida, Shola Emmanuel ya bayyana cewa fusatattun matasa a wajen sun dira kan direban kafin yan sanda suka kwacesa.

Yace:

"Kowa ya yi fushi saboda wannan ba shine karo na farko da hakan ke faruwa a Ilisan ba. Wadannan matasan tukin banza sukeyi; babu ruwansu. Sai da mutane suka kusa kona motar.

Wani dan'uwan yaran, Yomi Opeyemi, ya bayyana cewa an gurfanar da direban a kotu kuma an dage zaman zuwa ranar 27 ga Junairu.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun sake tare babbar hanya a Arewa, sun kashe mutane sun sace wasu 40

Yace:

“Moshood Gbadamosi ya gurfana gaban kotun majistare a Ikenne Remo ranar Litinin. Alkalin ya bada umurnin garkameshi. Kawai a hukuntashi; abinda muke bukata kenan."

An gama shirye-shiryen aure tsaf, kyakkyawar amarya tayi hadari ta mutu a Bauchi

A wani labari guda, ASP Abdulmuhyi Bagel Garba ya yi babban rashi a Duniya, yayin da wanda yake shirin ya aura a watan Fubrairun shekarar nan ta 2022 ta rasu.

Abdulmuhyi Bagel Garba jami’in ‘dan sanda ne wanda a watan gobe aka sa rai zai yi aure a Azare. Sai dai Allah (SWT) bai nufa zai auri masoyiyar ta sa ba.

Legit.ng Hausa ta samu labari cewa ASP Abdulmuhyi Bagel Garba kani ne ga kwamishinar wuta, kimiyya da fasaha ta jihar Bauchi, Maryam Garba Bagel.

Asali: Legit.ng

Online view pixel