An gama shirye-shiryen aure tsaf, kyakkyawar amarya tayi hadari ta mutu a Bauchi

An gama shirye-shiryen aure tsaf, kyakkyawar amarya tayi hadari ta mutu a Bauchi

  • A ranar 5 ga watan Fubrairu aka tsara Abdulmuhyi Bagel Garba zai auri Hauwa Abdullahi Shehu a Azare
  • Amma Allah (SWT) madaudakin Sarki bai nufa ASP Abdulmuhyi Bagel Garba zai auri wannan Baiwar Allah ba
  • Hauwa Abdullahi Shehu mai karatun ilmin Human Physiology a jami’ar Gadau ta rasu a hadarin mota

Bauchi - ASP Abdulmuhyi Bagel Garba ya yi babban rashi a Duniya, yayin da wanda yake shirin ya aura a watan Fubrairun shekarar nan ta 2022 ta rasu.

Abdulmuhyi Bagel Garba jami’in ‘dan sanda ne wanda a watan gobe aka sa rai zai yi aure a Azare. Sai dai Allah (SWT) bai nufa zai auri masoyiyar ta sa ba.

Legit.ng Hausa ta samu labari cewa ASP Abdulmuhyi Bagel Garba kani ne ga kwamishinar wuta, kimiyya da fasaha ta jihar Bauchi, Maryam Garba Bagel.

Tsohuwar ‘yar majalisar ta Bauchi, Maryam Garba Bagel ta fara bada labarum mutuwar Hauwa Abdullahi Shehu wanda aka fi sani da Ummi a Facebook.

Maryam Bagel tayi magana a Facebook

“Da ranar nan mu ka samu labari mai gigitarwa na mutuwar suruka ta, ‘Ummi’, wanda aka yi za ta auri ASP Abdulmuhyi Bagel, amma Allah bai nufa ba.”
“Allah ya yi mata rahama, ya ba ta Aljannah. Ameen.” - Maryam Bagel
Kyakkyawar amarya
Abdulmuhyi Bagel Garba da Hauwa Abdullahi Shehu Hoto: Instagram/LIB
Asali: Instagram

Hauwa Abdullahi Shehu ta cika

Linda Ikeji Blog ta fitar da rahoto cewa Hauwa Abdullahi Shehu ta na karatu ne a jami’ar jihar Bauchi da ke garin Gadau, ta na shekararta ta uku a makarantar.

Rahotanni sun bayyana cewa Ummi ta yi hadarin mota ne a ranar Lahadi, 2 ga watan Junairu, 2022 a hanyar komawa Gadau inda take karantar ilmin Physiology.

Bagel ya yi jimamin wannan rashi a shafinsa na Instagram, ya na mai yabon marigayiyar da har an buga katin auren shi da ita a ranar 5 ga watan Fubrairu, 2022.

Ango ya yi jimamin rashi

“A ranar 5 ga watan Fubrairu, 2022 ya kamata in yi murna a matsayin aurenmu na har abada, amma Allah (SWT) ya kaddara ba haka ba.”
“Shakka babu, ba a taba yin irinki ba. Allah ya hada mu a gidan Jannatul Firdausi. Allah ya jikanki masoyiyata.” - ASP Abdulmuhyi Bagel

Mutuwa masu ban tausayi

Kun ji cewa a ‘yan watannin bayan nan, an samu labarin masu shirin aure ko sababbin ma'auratan da suka riga mu gidan gaskiya a jihohin Najeriya.

A watan Nuwamban 2021 aka ji mutuwar Sani Ruba a hadarin mota a hanyar Yola. Ruba ya rasu ana saura makonni uku aurensa da Rafeeah Zirkarnain a Zaria.

Asali: Legit.ng

Online view pixel