Labari mai dadi: Gwamnatin Buhari ta hakura, an dage dokar hana Twitter

Labari mai dadi: Gwamnatin Buhari ta hakura, an dage dokar hana Twitter

  • Gwamnatin shugaba Buhari ta amince da dage dokar dakatarwar wucin gadi da ta sanya kan manhajar sadarwa ta Twitter
  • A baya gwamnatin Najeriya ta dakatar da Twitter saboda cire wani rubutu da shugaba Buhari ya yi a kafar a shekarar 2021
  • An dage dokar ne bayan ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Dr Isa Pantami ya ba Buhari wata takarda

Abuja - Gwamnatin tarayya ta dage dakatar da ayyukan kafar sadarwar Twitter a Najeriya bayan amincewar shugaban kasa Muhammadu Buhari, The Cable ta rahoto.

Shugaban Kwamitin Fasaha na Najeriya kan hulda da Twitter da Darakta Janar na Hukumar Bunkasa Fasahar Sadarwa ta Kasa (NITDA), Kashifu Inuwa Abdullahi, CCIE ne ya sanar da matakin dage dokar.

Shugaban NITDA ya sanar da dage dokar Twitter
Labari mai dadi: Gwamnatin Buhari ta hakura, an dage dokar hana Twitter | Hoto: dailynigerian.com
Asali: Facebook

Kashifu, a wata sanarwa da ya fitar a Abuja, ya ce an amince da hakan ne biyo bayan wata takarda da ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Farfesa Isa Ali Ibrahim ya rubuta wa shugaban kasa Buhari.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Yan a adaidaita sahu sun janye daga yajin aiki a jihar Kano

Jaridar The Nation ta ruwaito shi yana cewa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Gwamnatin tarayyar Najeriya (FGN) ta umurce ni da in sanar da jama’a cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari, GCFR, ya amince da janye dakatarwar da aka yi wa kamfanin Twitter a Najeriya daga karfe 12 na daren yau, 13 ga watan Janairu, 2022.
“An amince da hakan ne biyo bayan wata takarda da mai girma ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Farfesa Isa Ali Ibrahim ya rubutawa shugaban kasa.
"A cikin takardar, Ministan ya sabunta ya kuma nemi amincewar shugaban kasa don dage dokar bisa shawarar kwamitin fasaha na Najeriya kan Twitter."

FG zata dage dokar haramta Twitter, za a kafa ofishin Twitter a Najeriya

A wani labarin, Ministan yada labarai da al'adu, Lai Mohammed, ya bayyana cewa nan babu dadewa gwamnatin tarayya zata dage dokar haramta Twitter da tayi a Najeriya.

Kara karanta wannan

Sunaye: Rundunar sojin kasa ta yi girgiza, an sauya wa GOCs da manyan hafsoshi wurin aiki

Mohammed ya sanar da hakan ne bayan taron majalisar zartarwa ta kasa da suka yi ta yanar gizo wanda mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya jagoranta a fadar shugaban kasa dake Abuja.

A yayin bada bayanin sasancin gwamnati da Twitter, kamar yadda The Nation ta ruwaito, minsitan yace tuni Twitter ta amince da kusan dukkan sharuddan da Najeriya ta saka mata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel