Yanzu-yanzu: Yan a adaidaita sahu sun janye daga yajin aiki a jihar Kano

Yanzu-yanzu: Yan a adaidaita sahu sun janye daga yajin aiki a jihar Kano

  • Bayan kwana uku, matuka baburan a daidaita sahu sun yanke shawaran yanjewa daga yajin aiki
  • Shugaban hukumar KAROTA da wakilan kungiyar matukan sun bayyana hakan ga manema labarai

Jihar Kano - Masu kekuna mai kafa uku wanda aka fi sani da 'a daidaita sahu' a jihar Kano sun janye daga yajin aikin da suka tsunduma tun ranar Litinin.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa sun janye yajin aikin ne bayan dogon ganawar da aka yi tsakanin Dirakta Manajan hukumar KAROTA, Baffa Dan-Agundi da lauyoyin yan adaidaita sahu karkashin jagorancin Shugaban NBA, Aminu Gadanya.

Yanzu-yanzu: Yan a adaidaita sahu sun janye daga yajin aiki a jihar Kano
Yanzu-yanzu: Yan a adaidaita sahu sun janye daga yajin aiki a jihar Kano Hoto: Arewa Radio
Asali: Facebook

Yajin aikin yan a daidaita sahu

Kungiyar masu tuka a daidaita sahu ta jihar Kano ta bayyana kudurinta na fadawa yajin aiki ranar Litinin 10 ga watan Janairu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Yajin aikin 'yan adaidaita: PDPn Kano ta zargi Ganduje da shirin karya tattalin arzikin jihar

Wannan na zuwa ne bayan da kungiyar ta bayyana rashin jin dadinta ga yadda ake tafiyar da sana'ar a daidaita sahu a jihar.

Hakazalika, kungiyar ta koka kan yadda ake cin mutuncin masu sana'ar a jihar, inda kuma ta koka kan yadda mambobinta ke biyan haraji ba kan gado.

A cikin sanarwar da hukumar ta fitar wacce wakilinmu a Legit.ng Hausa ya gani, kungiyar ta bayyana wani gargadi ga mambobinta

Gwamnatin Kano tace zata samar da hanyar sufuri da za ta maye a daidaita sahu

Gwamnatin jihar Kano za ta sharewa mazauna jihar hawaye ta hanyar kaddamar da sabon tsarin sufuri biyo bayan yajin aikin 'yan a daidaita sahu, Daily Nigerian ta ruwaito.

Manajan daraktan hukumar KAROTA, Baffa Babba-Dan’agundi ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai kan yajin aikin da masu tuka a daidaita sahu a jihar suka yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel