FG zata dage dokar haramta Twitter, za a kafa ofishin Twitter a Najeriya

FG zata dage dokar haramta Twitter, za a kafa ofishin Twitter a Najeriya

  • Lai Mohammed, ministan yada labarai da al'adu yace nan babu dadewa gwamnatin tarayya zata dage dokar haramta Twitter
  • Mohammed ya sanar da cewa Twitter ta amince da dukkan sharuddan da aka gindaya mata a Najeriya
  • Ya kara da tabbatar da cewa kamfanin zai bude ofishi a Najeriya tare da ma'aikata da zasu kasance wakilanta a kasar nan

FCT, Abuja - Ministan yada labarai da al'adu, Lai Mohammed, ya bayyana cewa nan babu dadewa gwamnatin tarayya zata dage dokar haramta Twitter da tayi a Najeriya.

Mohammed ya sanar da hakan ne bayan taron majalisar zartarwa ta kasa da suka yi ta yanar gizo wanda mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya jagoranta a fadar shugaban kasa dake Abuja.

FG zata dage dokar haramta Twitter, za a kafa ofishin Twitter a Najeriya
FG zata dage dokar haramta Twitter, za a kafa ofishin Twitter a Najeriya. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC

A yayin bada bayanin sasancin gwamnati da Twitter, kamar yadda The Nation ta ruwaito, minsitan yace tuni Twitter ta amince da kusan dukkan sharuddan da Najeriya ta saka mata.

Kamar yadda yace, bangarorin da suka rage shine na kafa ofishin Twitter a Najeriya tare da daukar ma'aikata da zasu zama wakilan kasar kamar yadda suka tattauna.

Yaushe Twitter zata kafa ofishinta a Najeriya?

Mohammed ya bayyana cewa a bangaren kafa ofishin da Twitter zata yi a Najeriya, tace zata iya kaiwa zuwa farkon shekarar 2022 kafin ta kafa ofishin nata.

Minsitan ya bayyana tabbacin cewa za a kammala sasancin da Twitter cikin kwanaki kadan ko makonni, don haka 'yan Najeriya su kwantar da hankalinsu.

Ya ce kwamitin gwamnatin tarayya dake sasanci da twitter zasu sake haduwa kan yarjejeniyar da suka yi kafin a kammala komai, jaridar Daily Nigerian ta wallafa.

Gwamnatin tarayya ta haramta Twitter ne tun bayan da ta goge wata wallafa ta shugaban kasa Muhammadu Buhari.

EFCC ta titsiye tsohon gwamna a Najeriya, tana tuhumarsa

Rahotonni sun bayyana akan yadda jami’an EFCC suka hadawa tsohon gwamnan jihar Bayelsa, Sanata Seriake Dickson, zafi a ranar Talata, 10 ga watan Augusta.

Seriake ya sha tambayoyin kurar hali a gaban jami’an bayan ya bayyana a gaban jami’an bayan sun gayyaceshi.

An tattara bayanai akan yadda gwamnan mai wakiltar Bayelsa na yamma ya sha tambayoyi akan yadda ya tozarta ofishinsa ta hanyar wadaka da dukiyar al’umma na tsawon shekaru 8 da yayi mulki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel