Sunaye: Rundunar sojin kasa ta yi girgiza, an sauya wa GOCs da manyan hafsoshi wurin aiki

Sunaye: Rundunar sojin kasa ta yi girgiza, an sauya wa GOCs da manyan hafsoshi wurin aiki

  • Shugaban dakarun sojin kasa, Laftanal Janar Faruk Yahaya ya amince da nadi tare da sauya wa manyan dakarun sojoji wurin aiki don kara musu kaimi a kan ayyukansu
  • A wata takarda wacce darektan hulda da jama’an sojoji, Birgediya janar Onyeama Nwachukwu ya saki a Abuja, ya ce wannan nadin ya shafi kwamandoji da sauran manyan dakaru
  • A cikin takardar, Nwachukwu ya bayyana sunaye da kuma mukamai, da wuraren da aka tura kowanne soja a cikin hedkwatocin sojoji da ke fadin kasar nan

Shugaban rundunar sojin kasa, Laftanal Janar Faruk Yahaya, ya amince da nadi tare da sauya wa manyan sojojin kasa wuraren aiki duk don ba su kaimin yaki da ta’addanci a kasar nan.

A wata takarda wacce darektan hulda da jama’an soji, birgediya janar Onyema Nwachukwu ya saki a Abuja, ya ce wadanda lamarin ya shafa ya hada da kwamandoji da sauran manyan sojoji, Daily Nigerian ta ruwaito hakan.

Kara karanta wannan

Daga bisani, iyalan Shonekan sun bayyana abinda yayi sanadin mutuwarsa

Sunaye: Rundunar sojin kasa ta yi girgiza, an sauya wa GOCs da manyan hafsoshi wurin aiki
Sunaye: Rundunar sojin kasa ta yi girgiza, an sauya wa GOCs da manyan hafsoshi wurin aiki. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC

Nwachukwu ya ce an tura Manjo janar Godwin Umelo hedkwatar tsaro, DHQ daga cibiyar tsaro ta DSC a matsayin darekta janar na binciken harkokin tsaro da cigaban yaki, DRDB.

Ya kara da bayyana yadda aka tura Manjo Janar V Ebhaleme ya koma darektan Suport Service in Defence Space Administration yayin da Manjo Janar GB Audu ya koma Nigerian Army Resource Centre a matsayin babban ma’aikacin bincike.

Sauran wadanda abin ya shafa sun hada da kwamandan Kwalejin yaki ta sojojin Najeriya, Manjo Janar Solomon Udounwa wanda yanzu ya koma shugaban shirin sojoji na musamman a sabuwar Hedkwatar ayyuka na musamman na sojoji.

A cewarsa, an mayar da Manjo Janar MT Durowaiye daga hedkwatar sojoji ta tsare-tsare da shirye-shirye zuwa hedkwatar soji da kuma darektan harkokin tsofaffin soji.

Kara karanta wannan

Rundunar sojin Najeriya ta musanta hannun jami'anta a fada da masu hako zinari a Katsina

“Manjo janar AE ya koma Hedkwatar bangaren tsare-tsaren soji zuwa bangaren horarwar sojoji a matsayin darektan ayyukan tsaro yayin da Manjo Jamar UT Musa ya koma hedkwatar runduna ta 81 a matsayin kwamanda.
“Manjo Janar CU Onwunko ya koma darektan sadarwa na DHQ; Manjo Janar OO Oluyede ya koma Hedkwatar runduna ta 6 a matsayin kwamanda da kuma Manjo Janar LT Omoniyi ya koma hedkwatar rundunar soji na ayyuka a matsayin darektan tsare-tsare,” a cewarsa.

Mr Nwachukwu ya kara da bayyana yadda aka tura Manjo Janar OJ Akpor daga NDA zuwa hedkwatar tsaro a matsayin darektan labaran soji, yayin da aka mayar da Manjo Janar Abdulwahab Eyitayo ya koma runduna ta 6 zuwa hedkwatar tsaro a matsayin darektan tsare-tsare.

Ya kara da cewa, an mayar da Manjo Janar LA Fejokwu ya koma darektan tantancewa da tabbatar da tsari na DHQ, Manjo Janar JAL Jimoh ya koma makarantar sojoji ta Artillery zuwa hedkwatar horarwa ta TRADOC a matsayin shugaban horarwa.

Kara karanta wannan

Nasara daga Allah: Sojoji sun yi wa yan bindiga kwantan bauna, sun bude musu wuta a Kaduna

Ya ce manjo janar HT Wesley ya bar ofishin shugaban rundunar sojin kasa zuwa hedkwatar labarun sirri na soji a matsayin darektan ayyuka, sai manjo janar JO Ochai ya koma makarantar sojoji ta Armour a matsayin kwamanda.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa, ya kara da cewa an mayar da manjo janar SG Mohammed bangaren tsaro da ayyuka a matsayin mataimakin shugaba daga runduna ta 6 ta sojin Najeriya da sauransu.

“Cikin sauran wadanda abin ya shafa sun hada da birgediya janar AS Maikano ya koma kwamandan bangaren kudi da asusai daga bangaren inshora na walwalar soji.
“Birgediya janar LA Lebo ya zana zama mataimakin shugaban horarwa (Linkages/Integration) yayin da Birgediya janar MO Ihanuwaze ya koma darekta na kasafi da asusai (AHQ) da kuma birgediya janar Ojogbane Adegbe ya koma darektan Psychological Operation, fannin AHQ na harkokin Fararen hula da soji,” a cewar Nwachukwu.

Kakakin sojin ya bayyana yadda shugaban rundunar tsaro ta kasa, Laftanal Janar Faruk Yahaya, ya hori duk wadanda aka nada a sababbin mukamai da su jajirce su kara dagewa wurin yin ayyukansu.

Kara karanta wannan

Yadda Gwamna Zulum ya tallafawa sojoji ba tare da sun roke shi ba, GOC ya magantu

A cewarsa, COAS din ya yi kira gare su da su kasance masu yin ayyukansu yadda ya dace.

Asali: Legit.ng

Online view pixel