Ku daina rokon Buhari ya saki Nnamdi Kanu, Ohanaeze Ndigbo ga yan siyasa da dattawan Igbo

Ku daina rokon Buhari ya saki Nnamdi Kanu, Ohanaeze Ndigbo ga yan siyasa da dattawan Igbo

  • Ohanaeze Ndigbo ta ce yan siyasan Igbo da dattawan yankin Igbo su daina rokon Shugaba Muhammadu kan ya saki Nnamdi Kanu
  • Ohanaeze tace idan lokacin Allah yayi, za'a saki Nnamdi Kanu ba tare da wani matsala ba kuma zai samu nasara a kotu
  • Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa sam ba za sa baki cikin lamarin Nnamdi Kanu ba

Kungiyar kare hakkin yan kabilar Igbo a Najeriya, Ohanaeze Ndigbo, ta yi kira da yan siyasa da dattawan Igbo su daina rokon Shugaba Muhammadu Buhari ya saki Nnamdi Kanu.

Kungiyar tace yawancinsu munafukai ne kuma da saninsu aka kama Nnamdi Kanu tun daga farko, rahoton Guardian.

Nnamdi Kanu, wanda shine Shugaban kungiyar masu rajin kafa kasar Biyafara IPOB na daure hannun hukumar DSS tun bayan damkeshi a kasar Kenya.

Kara karanta wannan

Buhari ya tuno tsohuwar alaka, ya rabawa iyalin abokansa da suka mutu mukamai a NNPC

dattawan Igbo
Ku daina rokon Buhari ya saki Nnamdi Kanu, Ohanaeze Ndigbo ga yan siyasa da dattawan Igbo Hoto: Imo State Govt
Asali: Facebook

A jawabin da Sakataren Janar na ballin Chidi Ibeh na Ohanaeze, Mazi Okechukwu Isiguzoro, ya saki, ya ce babu gaskiya da iklasi cikin kiran da yan siyasan Igbo ke yi ga Shugaba Buhari ya saki Kanu.

A cewarsa:

"Munafukai ne, zasu yi ihu da safe amma da dare su shirya yadda zasu yi amfani da matashin wajen raya siyasarsu."
"Ohanaeze Ndigbo Worldwide na kira ga yan siyasan Igbo su daina rokon Shugaba Buhari bayan su suka taimaka aka kamashi."
"Asiri ya tonu cewa wasu Sanatoci da suka bada shawaran haramta kungiyar IPOB a 2017, ne suka fara kuka a saki Kanu."

Ya kara da cewa idan lokacin Allah yayi, za'a saki Nnamdi Kanu ba tare da taimakon yan siyasan ba.

Ba zan saki Nnamdi Kanu ba, ya kare kan shi a gaban kotu, Buhari

Kara karanta wannan

Ya kamata Igbo su bude zuciyarsu su fara yarda da Buhari, Kalu

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce shugaban 'yan awaren IPOB, Nnamdi Kanu, ya gurfana a gaban kotu tare da kare kansa a kan labaran karya da ya dinga yadawa a kasashen ketare kan mulkinsa.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce shugaban dan a waren IPOB, Nnamdi Kanu, ya kare kansa gaban kotu akan yada karairayi dangane da mulkinsa lokacin ya na kasashen ketare.

Buhari ya furta hakan ne yayin wata tattaunawa wacce gidan talabijin din Channels ta nuna a ranar Laraba kuma Legit.ng ta shaida.

Asali: Legit.ng

Online view pixel