Ya kamata Igbo su bude zuciyarsu su fara yarda da Buhari, Kalu

Ya kamata Igbo su bude zuciyarsu su fara yarda da Buhari, Kalu

  • Sanata Orji Uzor Kalu, ya shawarci mutanen yankin kudu maso gabashin Najeriya su bude zuciyarsu su rungumi Shugaba Buhari
  • Babban Bulaliyar na Majalisar Dattawa ya bayyana cewa ba gaskiya bane cewa Shugaba Muhammadu Buhari baya kaunar yankin kudu maso gabas
  • Kalu ya ce babu wani shugaban kasa kafin zuwan Buhari da ya yi wa yankin kudu maso gabas ayyukan tattalin arziki kamar Buhari yana mai cewa zai iya basu mamaki a gaba

Babban bulaliyar Majalisar Dattawa ta Najeriya, Sanata Orji Uzor Kalu ya shawarci 'yan Najeriya musamman kabilan Igbo su rika koya yadda za su rika yarda da Shugba Muhammadu Buhari, The Nation ta ruwaito.

Kalu, wanda ya yi magana a jiya a garinsu na Igbere yayin taron shugbannin OUK Movement da Reality Organisation a karamar hukumar Bende a jihar Abia ya ce ya kamata Igbo su amince kuma su yarda da Buhari.

Ya kamata Igbo su bude zuciyarsu su fara yarda da Buhari, Kalu
Ya kamata Igbo su fara yarda da Buhari, Kalu. Hoto: The Nation
Asali: Facebook

Tsohon gwamnan na jihar Abia, wanda ya bayyana shugaban kasar a matsayin shugaba mai kiyayye dokoki, ya ce akwai yiwuwar Buhari ya iya bawa Igbo mamaki (madadin zargin da galibinsu suke masa).

A cewar Kalu, Buhari ya fi yin manyan ayyuka na inganta tattalin arziki a kudu maso gabas fiye da dukkanin shugabannin kasa da suka gabace shi akasin zargin da ake yi na cewa Buhari bai damu da kudu maso gabas ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Buhari: PDP za ta kwace mulki daga hannun APC idan har bata magance rikice-rikicenta ba

A wani labarin, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ja kunne inda ya ce matsawar jam’iyyarsa, APC ba ta gyara duk wasu rigingimun da ke cikin ta ba, jam’iyyar adawa ta PDP za ta amshi mulki a shekarar 2023.

Shugaban kasa Buhari ya furta hakan ne yayin wata tattaunawa da aka yi da shi wanda NTA ta nuna ranar Alhamis da dare, Vanguard ta ruwaito.

Shugaban kasan ya kara da cewa ya yi takarar shugaban kasa har sau uku kafin ya samu nasara, don haka duk wani mai son zama shugaban kasa sai ya yi aiki tukuru a kan kudirinsa, rahoton Vanguard.

Asali: Legit.ng

Online view pixel