Da duminsa: Ba zan saki Nnamdi Kanu ba, ya kare kan shi a gaban kotu, Buhari

Da duminsa: Ba zan saki Nnamdi Kanu ba, ya kare kan shi a gaban kotu, Buhari

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce shugaban 'yan a waren IPOB, Nnamdi Kanu ya kare kansa a kotu bisa yada karairayin da ya yi akan mulkinsa lokacin yana kasar waje
  • Buhari ya bukaci jagoran 'yan waren IPOB, Nnamdi Kanu, da ya kare kansa a gaban kotu kan karairayin da ya dinga zugawa kan mulkinsa a duniya
  • Dama an samu bayanai akan yadda tsohon ministan sufurin jiragen sama, Chief Mbazulike Amaechi, ya je wurin shugaban kasar har fadarsa don rokon sakin Kanu

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce shugaban 'yan awaren IPOB, Nnamdi Kanu, ya gurfana a gaban kotu tare da kare kansa a kan labaran karya da ya dinga yadawa a kasashen ketare kan mulkinsa.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce shugaban dan a waren IPOB, Nnamdi Kanu, ya kare kansa gaban kotu akan yada karairayi dangane da mulkinsa lokacin ya na kasashen ketare.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Na shirya yin gaba da gaba da Tinubu a zaben fidda gwanin APC – Shahararren sanata

Buhari ya furta hakan ne yayin wata tattaunawa wacce gidan talabijin din Channels ta nuna a ranar Laraba kuma Legit.ng ta shaida shi.

Da duminsa: Ba zan saki Nnamdi Kanu ba, ya kare kan shi a gaban kotu, Buhari
Da duminsa: Ba zan saki Nnamdi Kanu ba, ya kare kan shi a gaban kotu, Buhari. Hoto daga Channelstv.com
Asali: UGC

Tun a baya, The Punch ta ruwaito yadda wasu manyan Ibo wadanda ministan sufurin jiragen sama na baya, Chief Mbazulike Amaechi, ya jagoranta suka kai wa shugaban kasa ziyara har fadarsa ta Aso Rock inda suka bukaci a saki Nnamdi Kanu.

Yayin ziyarar ta ranar 19 ga watan Nuwamban 2021, Buhari ya sanar da su cewa ba zai saka baki a lamarin shari’a ba amma ya ji nauyin bukatar da suka je da ita.

Yayin tattaunawar a ranar Laraba da dare, shugaban kasa yace:

“Akwai abinda ba zan taba sa baki akan shi ba, shari’a, kuma musamman shari’ar Kanu amma abinda ya fi ba ni mamaki shi ne yadda lokacin da Kanu ya ke a Turai ya na zagin gwamnati na yana surutai iri-iri, na sha zai iya zuwa ya kare kansa daga duk zargin da ya yi.

Kara karanta wannan

Yan Najeriya ne suka matsa sai dai Buhari ya yi takarar shugaban kasa, in ji Garba Shehu

“Don haka a yanzu muna ba shi damar kare kansa, ba ya je Turai yana surutai ba. Ya zo nan ya yi surutun da caccakar. ‘Yan Najeriya sun san ba na shiga harkar shari’a. Amma dangane da masu bukatar a sake shi, ba za mu iya sakin shi ba.”

Bayan an tambaye shi idan akwai mafita a siyasance, Buhari cewa ya yi akwai.

A cewarsa, idan kowa ya yi abinda ya dace, amma ba mutum ya je kasar waje ya dinga sukar matsalar tsaron kasar mu ba yana tunanin za a zura masa ido.

Don haka ya bukaci a bar Kanu ya fuskanci abinda ya janyo wa kansa.

Kanu, mai shekaru 54 dan asalin jihar Abia ne mutum na farko da aka kama a shekarar 2017 bayan ya bukaci ya raba yankin kudu maso gabas daga Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel