Da Dumi-Dumi: Yan bindiga sun sace matar mataimakin shugaban fadar gwamnati

Da Dumi-Dumi: Yan bindiga sun sace matar mataimakin shugaban fadar gwamnati

  • Wasu da ake zargin masu garkuwa ne sun sace matar mataimakin shugaban ma'aikatan gidan gwamnati a jihar Filato
  • Bayan wannan, yan bindiga sun sace daraktan ma'aikatar lafiya ta jihar Filato a wani hari na daban
  • Kakakin rundunar yan sandan jihar yace hukumar su ta dukufa wajen ceto matar, amma ba su samu rahoton sace Darakta ba

Plateau - Jaridar Punch ta rahoto cewa wasu yan bindiga sun yi garkuwa da Dorcas Vem, matar mataimakin shugaban ma'aikatan gidan gwamnatin Filato, Silas Vem.

Haka nan kuma, a wani harin na daban, yan bindiga sun sace Dakta Samuel Audu, daraktan ma'aikatar lafiya ta jihar Filato.

Majiyoyi daga fadar gwamnatin jihar Filato dake Jos, da kuma hedkwatar ma'aikatar lafiya sun tabbatar da faruwar lamarin ranar Talata.

Yan bindiga
Da Dumi-Dumi: Yan bindiga sun sace matar mataimakin shugaban fadar gwamnati Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Rahoto daga gidan gwamnatin jiha

Kara karanta wannan

Najeriya ta yi rashi: Tsohon shugaban kasa a Najeriya Ernest Shonekan ya rasu

Wata majiya daga fadar gwamnatin jihar Filato ta bayyana cewa:

"Kwana uku kenan ba'a san inda matar mataimakin shugaban ma'aikatan fadar gwamnati, Silas Vem, take ba. Ma'aikaciyar jami'ar Jos ce, mijinta kuma yana aiki a ofishin mataimakin gwamna."
"Matar tana cikin tafiya zata koma gida, wasu yan bindiga suka tare ta, suka tilasta mata fitowa daga motarta a gaban kofar gidan su, suka yi awon gaba da ita."

Majiyar ta kara da cewa lamarin ya faru ranar Lahadi, kuma tun wannan lokaci babu wanda ya sake ji daga gareta, kamar yadda Tribune Online ta rahoto.

Rahoto daga ma'aikatar lafiya

Wani ma'aikaci a ma'aikatar lafiya ta jihar, wanda ya tabbatar da sace Daraktan su, yace yana kan hanyar komawa gida bayan tashi daga aiki yayin da yan ta'addan suka sace shi a yankin Barkin Ladi.

Kara karanta wannan

Kaduna: Iyaye da malamai sun yi martani kan aikin kwana 4 na makarantun gwamnati

"A daren jiya Litinin, lamarin ya faru. Darakta yana da Asibitin kudi a karamar hukumar Barkin Ladi. Yana kan hanyar komawa gida bayan yaje kiran gaggawa a Asibiti yayin da yan bindigan suka afka masa."
"Yana cikin kiran matarsa ta bude masa kofa, lokacin yan bindigan suka tilasta masa shiga motarsu dake tsaye, suka tafi da shi."

Wane mataki yan sanda suka ɗauka?

Kakakin rundunar yan sandan jihar, Ubah Ogaba, da muka tuntube shi, yace hukumarsu na da masaniyar sace matar Mista Vem, kuma suna kokarin ceto ta.

Sai dai yace hukumar yan sanda ba ta da masaniya kan sace Darakta a Barkin Ladi, amma yace, "Ku bani lokaci zan neme ku bayan na bincika abin da ya faru a Barkin Ladi."

A wani labarin na daban kuma Sojoji sun yi wa yan bindiga kwantan bauna, sun bude musu wuta a Kaduna

Dakarun sojin Najeriya sun dakile wani hari kuma suka hallaka yan ta'adda biyar a kauyen Kwanan Bataro, karamar hukumar Giwa, jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

Allah ya yiwa uwargidar Janar Buba Marwa, Mrs Zainab, rasuwa

A bayanan da muka samu, sojojin na aikin sintiri a ƙaramar hukumar Giwa yayin da suka samu sahihin bayanin sirri na motsin yan bindiga zuwa garin Fatika.

Asali: Legit.ng

Online view pixel