Tinubu ya kai ziyarar jaje jihar Zamfara, ya bada gudunmuwar Milyan 50

Tinubu ya kai ziyarar jaje jihar Zamfara, ya bada gudunmuwar Milyan 50

  • Babban jigon jam'iyyar APC ya bada gudunmuwa ga iyalan wadanda aka kaiwa hari a jihar Zamfara
  • Wannan ya biyo bayan ziyarar tawagar da Shugaba Muhammadu Buhari ya tura jaje jihar Zamfara
  • Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle, ya mika godiyarsa bisa wannan ziyara da gudunmuwa

Tsohon Gwamnan jihar Legas, kuma jigon jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Bola Tinubu, ya bada gudunmuwan N50million ga iyalan wadanda aka kashe kwanakin nan a jihar Zamfara.

Tinubu ya bada wannan gudunmuwar ranar Alhamis yayinda ya kai ziyara jihar, rahoton Channels.

Asiwaju ya samu rakiyar tsohon gwamnan jihar Borno kuma Sanata mai wakiltar Borno ta tsakiya, Kashim Shettima.

Tinubu ya bada gudunmuwar Milyan 50
Tinubu ya kai ziyarar jaje jihar Zamfara, ya bada gudunmuwar Milyan 50 Hoto: Facebook
Asali: Facebook

Shugaba Buhari ya aike da tawagar wakilai Zamfara kan kashe mutane 200

Gabanin zuwan Tinubu, wakilan gwamnatin tarayya sun dira Gusau, babban birnin jihar Zamfara, ranar Laraba, domin jajantawa gwamnatin jihar bisa harin yan bindiga na kwanan nan.

Kara karanta wannan

Hotunan Buhari yayin da ya ziyarci iyalan Marigayi Shonekan don yi masu ta’aziyya

Punch ta rahoto cewa tawagar wakilan karkashin jagorancin Ministan tsaro, Bashir Magashi, ta kunshi, ministan ayyukan jin kai, Sadiya Umar Farouq, da kakakin Buhari, Malam Garba Shehu.

Sauran mambobin tawagar sun haɗa da, ministan harkokin yan sanda, Muhammad Dingyadi, mai bada shawara kan tsaro, Babagana Monguno, da kuma Sufeta janar na yan sanda, Usman Baba.

Yan bindiga sun kuma kai hari Zamfara, sun hallaka mutum 60

Mun kawo muku ranar 6 ga Junairu cewa akalla mutum 60 ake zargin an kashe yayinda yan bindiga suka kai hari wasu kauyukan jihar Zamfara.

Daily Trust ta ruwaito cewa kauyukan da aka kai hari sun hada da Kurfa Danya, Kurfa Magaji Rafin Gero, Tungar Isa da Barayar Zaki a karamar hukumar Bukkuyum da karamar hukumar Anka.

Kara karanta wannan

Allah ya yiwa tsohon shugaban UBEC, Farfesa Gidado Tahir na Jami'ar Abuja rasuwa

Wani mazaunin Zamfara mai suna Babangida yace sun yiwo tururuwa kan babura suna harbin yan gari suna kona gidaje da runbunan abinci. Mazaunan musamman mata da yara sun gudu da kafafuwansu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel