Allah ya yiwa Farfesa Gidado Tahir na Jami'ar Abuja rasuwa

Allah ya yiwa Farfesa Gidado Tahir na Jami'ar Abuja rasuwa

  • Mutumin farko da ya jagoranci hukumar raya kananan makarantu a Najeriya ya rigamu gidan gaskiya
  • Farfesan wanda yayi karatunsa a kasar Amurka ya mutu yana mai shekaru 73
  • Ya bar mata guda, Hajiya Asma'u Gidado, 'yaya da jikoki

Allah ya karbi rayuwar tsohon mataimakin shugaban jami'ar birnin tarayya Abuja, Farfesa Gidado Tahir, da daren Laraba, 12 ga Junairu, 2022.

Jami'ar Abuja ta sanar da mutuwarsa da safiyar Alhamis inda tayi addu'ar Allah ya jikansa da rahama.

Jawabin jami'ar:

"Yanzu muka samu labarin mutuwar tsohon mataimakin shugabanmu (DVC admin), Farfesa Gidado Tahir, mutum mai 'kankan da kai, malami da hazaka."
"Allah ya saka masa da Aljannah kuma ya karawa iyalai, abokai da yan'uwansa hakurin wannan rashi."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Tsagin shekarau ya sake yin nasara kan tsagin Ganduje a kotu

Allah ya yiwa Farfesa Gidado Tahir na Jami'ar Abuja rasuwa
Allah ya yiwa Farfesa Gidado Tahir na Jami'ar Abuja rasuwa Hoto: Umar Liman
Asali: Facebook

Ya karantar a jami'ar Usman Dan Fodio dake Sokoto da Jami'ar Abuja, inda ya rike matsayin mataimakin shugaban jami'a kafin yayi ritaya.

An haifeshi a ranar 29 ga Disamba, 1949 a garin Toungo, jihar Adamawa.

Ya kasance Shugaban kwalejin ilimin Yola tsakanin 1987 da 1994, ya kasance shugaban majalisar jagorancin hukumar ilmin kiwo kuma ya rike kujerar shugaban hukumar kananan makarantun Najeriya.

Ya bar mata guda, Hajiya Asma'u Gidado, 'yaya da jikoki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel