Karon farko, an samu nasarar yiwa dan Adam dashin zuciyar Alade a Amurka

Karon farko, an samu nasarar yiwa dan Adam dashin zuciyar Alade a Amurka

  • An sake samun nasarar yiwa dan Adam dashin sashen jikin Alade kuma ya zauna daram babu matsala
  • A baya mun kawo muku yadda aka yiwa wani mutum dashin kodar Alade kuma yayi masa aiki
  • Wannan karon a Amurka, an dasawa wani mutum zuciyar Alade kuma ya farka yana murmurewa

Karon farko a tarihi, Likitoci sun samu nasarar yiwa dan Adam dashin zuciyar Alade a jikin wani mutumin da aka fidda rai zai rayu.

Mutumin da aka yiwa dashin, David Bennet Sr, a birnin Maryland, kasar Amurka yana kwance yanzu yana murmurewa kawo ranan Litinin a asibitin jami'ar Maryland.

Diraktan dashin zuciya a asibitin, Dr Bartley Griffith, ya bayyanawa New York Times cewa:

"Tana bugawa, tana bada iskar da ake bukata, zuciyarsa ce kawai. Tana aiki sosai, mun ji dadi, amma bamu san abinda zai faru gobe ba. Ba'a taba irin wannan ba."

Kara karanta wannan

Tiwa Savage: Na so ace Dangote mahaifi na ne, amma kash

Dashin zuciyar Alade a Amurka
Karon farko, an samu nasarar yiwa dan Adam dashin zuciyar Alade a Amurka Hoto: University of Maryland School of Medicine
Asali: UGC

Wannan shine karo na farko da za'a yiwa mutum dashin zuciyar dabbar da aka kirkira kimiyance wato 'Genetically Modified' ba tare da wata matsala ba, a cewar UMD.

Mutumin da aka yiwa dashin yace:

"Aikin tiyatan fa ko rai ko mutuwa ne. Ina son in rayu. Na san da kamar wuya, amma shine zabin da nake da shi. Ina kyautata zaton warkewa gaba daya."

Likitoci sun samu nasarar dasawa dan Adam kodar Alade a Amurka

A baya mun kawo muku cewa an samu nasarar dasa kodar Alade cikin dan Adam ba tare da wata matsala ba, wani sabon bincike da ka taimakawa mutane masu matsalar cutar koda.

Reuters ta ruwaito cewa an gudanar da wannan aiki ne a jami'ar New York dake kasar Amurka.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: 'Yan bindiga sun sace fasinjoji a Imo yayin da suka hanyar zuwa Legas

An yi amfani da kwayar hallitar Aladen da aka canza ne bayan cire wani kwaya wanda zai iya kawo matsala jikin mutum, binciken ya nuna.

An gwada wannan bincike ne kan mara lafiyar da kwakwalwarta ta mutu kuma take fama da ciwon koda bayan amincewar iyalansa, masu binciken suka bayyanawa Reuters.

Tsawon kwanaki uku, an dasa sabon kodar cikin jininta amma ba'a dinke ba domin ganin yadda abun zai gudana.

Asali: Legit.ng

Online view pixel