Yanzu-Yanzu: Bayan shekaru 10, Buni ya janye dokar hana hawa babur a Yobe

Yanzu-Yanzu: Bayan shekaru 10, Buni ya janye dokar hana hawa babur a Yobe

  • Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni ya sanar da janye dokar hana hawa babura da aka saka a wasu kananan hukumomi 10 a Jihar tun shekaru 10 da suka gabata.
  • Buni ya sanar da janye dokar ne a lokacin da ya kai ziyara fadar Sarkin Nguru domin jajantawa mutanen garin bisa iftila'in da ya faru a kasuwar Nguru
  • Gwamna Buni ya ce an janye dokar ne saboda an samu zaman lafiya da tsaro a garuruwan da a baya hare-haren Boko Haram yasa aka saka dokar a Janairun 2012

Jihar Yobe - Gwamna Mai Mala Buni na Jihar Yobe ya janye dokar hana hawa babur a kananan hukumomi 10 na Yobe North da South a Jihar, Daily Trust ta ruwaito.

Buni ya bada sanarwar ne a fadar sarkin Nguru yayin da ya tafi yi wa mazauna garin jaje bisa iftila'in da ya faru a kasuwar Nguru.

Kara karanta wannan

Allah ya yiwa uwargidar Janar Buba Marwa, Mrs Zainab, rasuwa

Yanzu-Yanzu: Bayan shekaru 10, Buni ya janye dokar hana hawa babur a Yobe
Gwama Buni ya janye dokar hana hawa babur a Yobe baya shekaru 10. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Buni ya ce a yanzu mazauna garin suna iya cigaba da amfani da baburansu su tafi gonakinsu da wasu wurare kamar yadda suka saba.

Dalilin janye dokar

Buni ya bayyana cewa an dauki sabon matakin janye dokar ne saboda samun cigaba a bangaren tsaro a yankunan kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Gwamnatin Jihar Yobe ta haramta amfani da babura ne a lokacin da hare-haren kungiyar Boko Haram ta yi kamari a watan Janairun 2012.

Sakamakon hakan ne gwamnati ta hana amfani da babura a kananan hukumomi da suka hada da Bade, Nguru, Karasuwa, Yusufari, Machina, Jakusko, Fune, Fika, Nangere and Potiskum.

'Daya daga cikin ɗaliban Jihar Yobe da gwamna ya ɗauki nauyin karatunsu ya rasu a Indiya

A wani labarin daban, kun ji cewa daya daga cikin daliban da gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya dauki nauyin karatunsu ya kwanta dama a kasar Indiya, inda ya ke karatun.

Kara karanta wannan

Matawalle ya magantu kan sabon harin Zamfara, ya ce za a tura manyan jiragen yaki jihar

Dalibin, Galadima Bulama, wanda ya ke karatu a fannin gwaje-gwajen lafiya a wata jami’a da ke Indiya ya rasu ne ranar Alhamis, 6 ga watan Janairun 2022, kamar yadda Sheriff Almuhajir ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Almuhajir jagora ne a cibiyar da Gwamna Buni ya kafa don daukar nauyin dalibai musamman marayu masu hazaka da ke jiharsa don ketarawa da su kasashen waje su yi karatu a fannoni daban-daban.

Kamar yadda Almuhajir ya wallafa, Bulama dan asalin Kauyen Bularafa ne da ke karkashin karamar hukumar Gulani cikin jihar. Kuma maraya ne da ke karkashin kulawar kanin mahaifinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel