'Daya daga cikin ɗaliban Jihar Yobe da gwamna ya ɗauki nauyin karatunsu ya rasu a Indiya

'Daya daga cikin ɗaliban Jihar Yobe da gwamna ya ɗauki nauyin karatunsu ya rasu a Indiya

  • Allah ya yiwa daya daga cikin tarin daliban da gwamna Mai Mala Buni ya dauki nauyin karatunsu, Galadima Bulama rasuwa a kasar Indiya, inda ya ke karatu
  • Bulama dan asalin karamar hukumar Gulani ne da ke jihar, kuma maraya ne wanda ya samu nasarar lashe jarabawa har ya fara karatu a fannin gwaje-gwajen lafiya a kasar wajen
  • Sheriff Almuhajir, wanda jagora ne a cibiyar da gwamna Buni ya kafa don daukar nauyin karatun daliban ya wallafa mutuwar a shafinsa na Facebook ranar Alhamis da safe

Daya daga cikin daliban da gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya dauki nauyin karatunsu ya kwanta dama a kasar Indiya, inda ya ke karatun.

Dalibin, Galadima Bulama, wanda ya ke karatu a fannin gwaje-gwajen lafiya a wata jami’a da ke Indiya ya rasu ne ranar Alhamis, 6 ga watan Janairun 2022, kamar yadda Sheriff Almuhajir ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

Zamfara: 'Yan daba sun kai farmaki gidan talabijin, sun raunata edita tare da lalata kayan aiki

'Daya daga cikin ɗaliban Jihar Yobe da gwamna ya ɗauki nauyin karatunsu ya rasu a Indiya
Allah ya yi wa daya cikin daliban Jihar Yobe da gwamna ya dauki nauyin karatunsu rasuwa Indiya. Hoto: Sheriff Almuhajir
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Almuhajir jagora ne a cibiyar da Gwamna Buni ya kafa don daukar nauyin dalibai musamman marayu masu hazaka da ke jiharsa don ketarawa da su kasashen waje su yi karatu a fannoni daban-daban.

Dan asalin Karamar Hukumar Gulani ne

Kamar yadda Almuhajir ya wallafa, Bulama dan asalin Kauyen Bularafa ne da ke karkashin karamar hukumar Gulani cikin jihar. Kuma maraya ne da ke karkashin kulawar kanin mahaifinsa.

Ya ce yana daya daga cikin daliban da su ka yi jarabawar tantancewa kuma ya samu nasara yanzu haka dalibi ne da ke karantu a fannin gwaje-gwajen lafiya, ya na aji na biyu.

Kamar yadda ya wallafa:

“Abinda ya burge ni a rayuwar wannan yaro shi ne; mun samu shaidar cewa cikin kudin abinci da gwamnatin Yobe ta ke aika masa duk wata, ya na ware wani bangare wurin tallafa wa mahaifiyarsa don kulawa da kanninsa.”

Kara karanta wannan

Jigon APC ya yaba da aikin Buni, ya ba da shawara kan shirin zaben 2023 ga Buhari

A hanyarsa ta komawa gida daga makaranta ya fadi ya ji ciwo

Ya shaida yadda wayar matashin ta lalace wanda hakan ya kange sa daga samun damar magana da iyayensa. Sai dai bayan ya samu rauni a hanyarsa ta komawa gida kwana biyu da sanar da iyayensa hakan ya fadi kasa ya ji ciwo.

Almuhajir ya ce an garzaya da Bulama asibitin koyarwa na jami’ar Glocal da ke cikin jami’ar da ya ke karatu daga nan ya koma ga mahaliccinsa.

Gwamnatin jihar Yobe ta bukaci yin ta’aziyyarsa a Indiya

Tuni gwamnatin jihar Yobe ta nemi izinin iyayensa don su amince a yi jana’izarsa a yankin Saharanpur da ke Indiya bayan ganin kewaye wurin ya ke da musulmai.

Daga karshe ya mika ta’aziyyarsa ga iyayen mamacin, hukuma, abokansa da daukacin al’ummar Jihar Yobe bisa wannan babban rashi.

Ya yi masa fatan samun Aljannah a matsayin makomarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel