Tashin hankali: 'Yan sanda sun shiga tsakani yayin da kwarto ya kashe mijin daduronsa

Tashin hankali: 'Yan sanda sun shiga tsakani yayin da kwarto ya kashe mijin daduronsa

  • ‘Yan sanda sun kama Daniel Udoh mai shekaru 38 a jihar Ogun bisa laifin kashe mijin daduronsa Emaka Umonko
  • Umonko dai ya fuskanci Udoh ne bayan zargin cewa akwai soyayya tsakanin mutumin da matarsa da ba a bayyana sunanta ba
  • Rikicin ya rikide zuwa mummunan fada, inda Udoh ya caka ma marigayin wuka sau da yawa a bayansa da kirjinsa

Onipanu, Ogun - Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi, ne ya bayyana hakan ta wata sanarwa a ranar Lahadi, inda ya bayyana wanda aka kashen a matsayin Emaka Umonko, mijin wata mata da ake zargin tana soyayya da Daniel.

Ya ce an kama wanda ake zargin ne biyo bayan kiran da ofishin DPO na Onipanu ya samu, gidan talabijin na Channels ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Mummunar gobara ta yi kaca-kaca da wani gida, uwa da jaririnta sun kone a Kano

Mutumin da ya kashe mijin daduronsa
Tashin hankali: Wani kwarto ya kashe mijin daduronsa, 'yan sanda sun shiga tsakani | Hoto: pmnewsnigeria.com
Asali: UGC

A cewar kakakin ‘yan sandan, marigayin ya dade yana zargin cewa Udoh na alaka da matars, wanda daga nan ya tunkare shi, lamarin da ya kai ga kazamin fada tsakanin mutanen biyu.

SaharaReporters ta ruwaito sanarwar na cewa:

"A yayin da ake ci gaba da gwabzawa, wanda ake zargin wanda direba ne, ya fito da wuka ya kuma yi amfani da ita wajen daba wa marigayin da dama a bayansa da kuma kirjinsa, daga nan ne marigayin ya fadi."

Sanarwar ta ce, tuni dai DPO din ya tura jami'ansa domin su ga yadda lamarin ya faru da kuma kamo wanda ake zargin.

An garzaya da wanda aka kashe, wanda ke sana'ar walda, zuwa Asibitin Jihar Ota, amma abin takaici Likitan da ke bakin aiki ya ce ya mutu.

Kara karanta wannan

Gwamnatina ba za ta yi watsi da ku ba: Shugaba Buhari ya yi jajen kisan 'yan Zamfara

Daga baya aka ajiye gawarsa a dakin ajiye gawa na babban asibitin Ifo domin ci gaba da bincike.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Ogun, Lanre Bankole, ya bayar da umarnin a mika wanda ake zargin zuwa sashin binciken manyan laifuka da leken asiri na jihar, domin ci gaba da bincike.

Rahotanni sun ce za a gurfanar da shi gaban kotu da zarar an kammala bincike.

Matashi ya biya abokinsa N100,000 ya kashe mahaifinsa saboda ya gaji da jiran gado

A wani labarin, rundunar ‘yan sandan Najeriya na reshen jihar Neja sun kama wani matashi mai suna Abubakar Mohammed Buba da laifin kashe mahaifinsa.

Jaridar Punch tace ‘yan sanda na zargin wannan matashi Abubakar Mohammed Buba mai shekara 25 da hannu wajen hallaka tsohon da ya haife shi.

Ana tuhumar Abubakar Mohammed Buba da biyan wani abokinsa kudi N110, 000 domin ya kashe mahaifinsa, wannan ya faru ne a Chachanga, a jihar Neja.

Kara karanta wannan

Wani mutum ya dawo daga kasar waje, ya tarar wani yana gina katafaren gida a filinsa, mutane sun magantu

Asali: Legit.ng

Online view pixel