Dalilin da yasa muke zaune lafiya, ba rikicin addini ko kabilanci a Kano, Ganduje

Dalilin da yasa muke zaune lafiya, ba rikicin addini ko kabilanci a Kano, Ganduje

  • Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano yace Allah ne kaɗai zai iya tabbatar da zaman lafiya da tsaro a Najeriya
  • Ganduje ya kuma bayyana cewa jiharsa ta tsira daga rikicin addini ko kabilanci ne saboda addu'a da kuma haɗin kan jami'an tsaro
  • Shugaba Buhari, ya yaba wa gwamna Ganduje, bisa kokarin da yake na tabbatarbda tsaro ta hanyar shirya addu'o'i na musamman

Kano - Gwmanan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, yace ba'a samun rikicin addini ko kabilanci a jihar ne saboda addu'a da kuma haɗin kai tsakanin hukumomin tsaro.

Ganduje ya yi wannan furuscin ne a filin wasa na Sani Abacha, jihar Kano, inda aka gudanar da addu'ar neman zaman lafiya da tsaro a ƙasa, ranar Asabar, kamar yadda Dailytrust ta ruwaito.

Gwamnan Kano, Ganduje
Dalilin da yasa muke zaune lafiya, ba rikicin addini ko kabilanci a Kano, Ganduje Hoto: Aminu Dan Almajiri
Asali: Facebook

Gwamnan ya roki jagoran Ɗarikar Tijjaniya a Najeriya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, wanda ya samu halartar taron, cewa su kawo Mauludin Sheikh Ibrahim Nyass, jigar Kano.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari ya sake caccakar majalisun tarayya kan sabon kundin zabe a tattaunar yau

Allah ne kaɗai zai iya tabbatar da tsaro - Ganduje

Ganduje, ya yabawa kokarin shugaban ƙasa Buhari, wajen kokarin kawo tsaro amma ya jaddada cewa Allah ne kaɗai zai iya tabbatar da zaman lafiya da tsaro, dan haka akwai bukatar addu'a.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Dakta Abdullahi Ganduje, ya bada tabbacin cewa gwamnatin jihar Kano zata cigaba da shirya addu'o'i duk shekara.

Muna bukatar addu'a - Buhari

Da yake jawabi a wurin taron, Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, yace yaƙi da matsalar tsaro a Najeriya ba zata yuwu ba sai da taimakon Allah da kuma amincewarsa.

Buhari, wanda ƙaramin ministan noma, Mustapha Baba Shehuri, ya wakilta, yace gwamnatin ba zata huta ba a kokarin da take na tabbatar da zaman lafiya a ƙasa baki ɗaya.

Shugaban ya kuma yaba wa gwamna Ganduje, bisa ɗaukar matakin dawo da zaman lafiya a Najeriya, ta hanyar shirya taron addu'a na ƙasa.

Kara karanta wannan

Matan Arewa sun bayyana sunan gwamnan da suke kaunar ya gaji Buhari a zaben 2023

"Muna kira ga al'ummar jihar Kano, su baiwa gwamnatin Ganduje goyon baya domin sai da tsaro ne za su samu damar amfana da ayyukan cigaba a jihar."

A wani labarin na daban kuma mun kawo muku hakikanin abin da ya kai Goodluck Jonathan wurin shugaba Buhari sau 2 a kwana 7

Sabon rikici na neman barkewa a jam'iyyar APC mai mulki game da ziyarar tsohon shugaban ƙasa Jonathan zuwa wurin Buhari.

Wasu na kallon abun akwai wata manaƙisa a ƙasa, yayin da wasu ke ganin APC na son tsayar da Jonathan takara ne a 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel