Bikin Maulidi Na Duniya: Yahaya Bello Ya Tarbi Niasse, Sanusi Da Manyan Malaman Musulunci a Kogi

Bikin Maulidi Na Duniya: Yahaya Bello Ya Tarbi Niasse, Sanusi Da Manyan Malaman Musulunci a Kogi

  • Birnin Lokoja ta Jihar Kogi ta cika ta batse a yayin da Gwamna Yahaya Bello ke tarbar bakuncin Sheikh Ibrahim Niasse, Alhaji Muhammdu Sanusi da wasu manyan malamai
  • Malaman na addinin musulunci tun dira birnin na Kogi ne domin bikin Maulidi na duniya na bana da aka yi a birnin na Lokoja da ke Jihar Kogi inda Gwamna Yahaya ne mai masaukin baki
  • Ana sa malaman addinin musulunci musamman na darikar Tijjaniya ne daga sassan duniya daban-daban za su hallarci taron Maulidin inda za a gabatar da kasidu da wa'azi da zikiri da walima

Lokoja - Yahaya Bello ya karbi bakuncin Mai Girma, Shiekh Ibrahim Niasse, Babban Khalifa na Jamiyyatu Ansarideen (Attijaniya) da Alhaji Muhammadu Sanusi, wanda shine shugaban Jamiyyatu Ansarideen (Attijaniya) na duniya.

Kara karanta wannan

Innalillahi wa inna ilaihi raji'un: Fitaccen Shehin Tijjaniyya a Najeriya ya rigamu gidan gaskiya

Gwamnan na Kogi ya tarbe su tare da wasu manyan malaman addinin musulunci a yayin da jiharsa ke daukan nauyin bikin Maulidi na duniya na kasa a bana, Daily Trust ta ruwaito.

Bikin Maulidi Na Duniya: Yahaya Bello Ya Tarbi Niasse, Sanusi Da Manyan Malaman Musulunci a Kogi
Maulidi Na Duniya: Yahaya Bello Ya Tarbi Sanusi Da Sauran Manyan Malaman Musulunci a Kogi. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa, NAN, ta rahoto cewa, an yi taron ne a Lokoja, babban birnin jihar Kogi daga ranar 6 zuwa 8 ga watan Janairun 2022 da aka yi wa lakabi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ana bikin Maulidi ne domin karrama Annabi Mohammad (SAW), wacce kungiyar Jamiyyatu Ansariddeen (Attijaniyya) ta ke yi karkashin jagorancin Shiekh Niasse.

Ana sa ran taron zai gayyato malaman addinin musulunci daga kasashe daban-daban domin su gabatar da kasida kan koyarwar Annabin Tsira (SAW) da suka shafi halin da al'umma suka tsinci kansu a yanzu.

Yayin bikin Maulidin, za a kai ziyara ga marasa lafiya asibitoci daban-daban a jihar, sannan a yi walimar cin abinci na musamman don karrama Annabi Muhammad (SAW).

Kara karanta wannan

2023: Ƙungiyar arewa ta bayyana sanata daga kudu da ta ke son ya gaji Buhari

Za kuma a yi Zikirin ranar Juma'a a babban masallacin Lokoja kamar yadda aka saba yi a rana irin wannan.

Khalifan Tijjaniyya na duniya da sauran manya sun wuce taron Zikirin da SLS ya shirya, sunki zuwa na Ganduje

A baya kun ji cewa, Khalifan Tijjaniyya na duniya, Sheikh Mahy Niasse da sauran manyan shugabannin Tijjaniyya sun ki zuwa taron zikiri wanda gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya shirya a fadar sarkin Kano, Daily Nigerian ta ruwaito.

Zikiri taro ne wanda malamai sufaye su ke yi don addu’o’i, kuma ana sa ran za ayi shi ne a ranar Juma’a.

Majiyoyi sun ce taron na Kano ya zo rana daya da wani zikiri na Lokoja wanda sabon shugaban darikar Tijjaniyyar na Najeriya kuma tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sunusi II ya shirya.

Majiyoyi daga ciki sun sanar da Daily Nigerian cewa gwamnatin jihar Kano da masarautar Kano ne su ka shirya duk don su kaskantar da mulkin Sunusi a kungiyar kuma don su samar da rabuwar kawuna cikin masu matsayi a Tijjaniyya.

Kara karanta wannan

Fusatattun matasa sun farmaki manyan sarakunan jihar Bauchi

Asali: Legit.ng

Online view pixel