Ortom ga FG: Ku ayyana Miyetti Allah a matsayin kungiyar ta'addanci

Ortom ga FG: Ku ayyana Miyetti Allah a matsayin kungiyar ta'addanci

  • Samuel Ortom, gwamnan jihar Binuwai ya bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ayyana kungiyar makiyayan shanu ta Miyetti Allah a matsayin kungiyar ‘yan ta’adda
  • Wannan kiran na gwamnan ya biyo bayan ayyana 'yan bindiga matsayin 'yan ta'adda da gwamnatin tarayya ta yi kuma gwamnatin ta ce babu wani daga kafa
  • Gwamnan ya yi kara ga 'yan Najeriya da su koma yin PDP saboda ita kadai ce za ta ceto su daga bakar wahala tare da mugun mulkin da suke ciki

Benue - Gwamnan jihar Binuwai, Samuel Ortom ya yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya ayyana kungiyar makiyayan shanu ta Miyetti Allah, MACBAN, a matsayin kungiyar ‘yan ta’adda.

Kiran ya biyo bayan yadda gwamnatin tarayya ta ayyana ‘yan bindiga a matsayin ‘yan ta’adda, TheCable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

An samu sauyi: Bayan ayyana 'yan bindiga a matsayin 'yan ta'adda, Buhari ya bayyana yadda zai yake su

A wata takarda wacce sakataren watsa labaran gwamnan, Nathaniel Ikyur ya saki, ya yanko inda gwamnan ya ce kungiyar tana kawo tashin hankali a Binuwai.

Ortom ga FG: Ku ayyana Miyetti Allah a matsayin kungiyar ta'addanci
Ortom ga FG: Ku ayyana Miyetti Allah a matsayin kungiyar ta'addanci. Hoto daga Daily Trust
Asali: Facebook
“Da alamu matakan da gwamnatin tarayya za ta dauka a kan ‘yan bindiga masu karfi ne, kuma tsaro zai inganta matsawar aka yi abubuwan da su ka dace idan har ta yi hakan a kan kungiyar makiyayan shanu ta Miyetti Allah, MACBAN da kungiyar Fulani ta kasa (FUNAM) saboda yadda su ke tayar da hankula a jihar Binuwai sakamakon dokar hana budadden kiwo,” kamar yadda takardar ta zo.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Ga mu ‘yan jihar Binuwai, dokar ta zo ne don ta tsaya. Ba za a taba sauya ta ba. Ba za a taba bayar da damar ci gaba da kiwo a budadden wuri ba.
“An saka dokar ne don kawo zaman lafiya da tsaro a jihar, kuma hakan zai rage rikicin makiyaya da manoma a jihar

Kara karanta wannan

Daga Karshe: Gwamnati Buhari amince da ayyana 'yan bindiga a matsayin 'yan ta'adda

“Yan Najeriya sun sha wahalar bakar yunwa da fatara a hannun bakin mulkin APC. Shin zai iya yuwuwa shugaban kasa ya ce bai san ‘yan Najeriya su na wahala sakamakon bakin mulkinsa ba ne?”

TheCable ta ruwaito cewa, Ortom ya hori ‘yan Najeriya da su goyi bayan PDP.

“A shirye PDP ta ke da ta ceci Najeriya daga rashin tsaro da tabarbarewar tattalin arzikin da APC ta tsoma ‘yan Najeriya,” a cewarsa.

Ya kara da cewa jam’iyyar ta kammala shirye-shirye don samar da walwalar ‘yan Najeriya da bunkasa kasar daga tatsuniyoyin APC.

2023: Najeriya na bukatar wanda zai kawo hadin kai kamar Atiku, Dokpesi

A wani labari na daban, Raymond Dokpesi, tsohon shugaban kafar sadarwa ta Daar ya ce ya kamata shugaban kasan da zai gaji mulki a 2023 ya kasance wanda zai hade kan kasar, TheCable ta ruwaito.

Dokpesi ya ce Najeriya ba ta taba rabuwa ba, inda ya kara da cewa kasar nan ta na bukatar mutum kamar Atiku Abubakar ne, tsohon mataimakin shugaban kasa, ya mulki kasar yadda ya dace.

Kara karanta wannan

Matan Arewa sun bayyana sunan gwamnan da suke kaunar ya gaji Buhari a zaben 2023

Asali: Legit.ng

Online view pixel