Innalillahi: 'Yan bindiga sun dasa bama-bamai a ofishin 'yan sanda, sun saki masu laifi

Innalillahi: 'Yan bindiga sun dasa bama-bamai a ofishin 'yan sanda, sun saki masu laifi

  • Wasu 'yan bindiga sun farmaki wani yankin jihar Imo, inda suka lalata ofishin 'yan sandan yankin
  • Hakazalika, sun saki mutane da dama da aka tsare a ofishin 'yan sanda bayan aikata mummunan barna
  • Ya zuwa yanzu, kakakin rundunar 'yan sandan jihar ya ce batun bai zo gabansa ba, amma dai yana jiran bayanai

Jihar Imo - A ranar Alhamis ne wasu ‘yan bindiga suka dasa bam a hedikwatar ‘yan sandan karamar hukumar Ideato ta Kudu da ke Dikenafai a jihar Imo.

Sun saki mutanen da aka tsare a ofishin na 'yan sanda, inji rahoton jaridar The Nation.

Maharan wadanda suka zo da yawa sun banka wa wani bangare na ofishin ‘yan sandan wuta da bama-bamai.

'Yan bindiga sun yi barna a jihar Imo
Da dumi-dumi: 'Yan bindiga sun dasa bam a ofishin 'yan sanda, sun saki masu laifi | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Bama-baman sun lalata ofishin gudanarwa, ofishin jami’an ‘yan sanda na shiyya, da kuma ofishin karbar baki.

Kara karanta wannan

Ka yi daidai: Shehu Sani ya goyi bayan Buhari kan watsi da batun 'yan sandan jiha, ya fadi dalili

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shugaban kwamitin riko na karamar hukumar Ideato ta kudu Fasto Bede Ikeaka ya bayyana kaduwarsa da faruwar wannan mummunan lamari.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Imo, Michael Abattam, ya ce har yanzu ba a yi masa bayani kan harin ba.

Ya yi alkawarin ba da bayanai idan batun yazo gabansa.

An samu labarin cewa wasu ‘yan banga na yankin sun kama wasu daga cikin wadanda ake tsare da su da suka tsere.

A wani rahoton na P.M News, ‘yan bindigar da suka zo da yawa sun lalata ginin da bama-bamai.

'Yan bindiga sun kone kauyuka 5 kurmus, sun hallaka mutane a Zamfara

A wani labarin, daruruwan mazauna kauyuka biyar ne a kananan hukumomin Anka da Bukkuyum na jihar Zamfara suke ta tururuwa zuwa cikin garin Anka bayan da ‘yan bindiga suka kashe mutane da dama a kauyukansu.

Kara karanta wannan

Yan ta'addan ISWAP su kai wani mummunan hari mutane na tsaka da Sallah a jihar Yobe

Majiyoyi da suka zanta da jaridar Premium Times sun ce har yanzu ba a tantance adadin wadanda aka kashe ba.

Wani lauya wanda kuma mamba ne a kungiyar agaji ta Zamfara, ya ce ya ga yawancin mutanen kauyen da suka rasa matsugunai a sakateriyar karamar hukumar Anka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel