Tashin Hankali: Wasu bakin mutane akalla 600 sun shiga wata jiha a Arewa a Tirela biyu

Tashin Hankali: Wasu bakin mutane akalla 600 sun shiga wata jiha a Arewa a Tirela biyu

  • Mutane sun shiga tashin hankali yayin da wasu baƙi mutum 600 suka shiga kauyen Maihula dake karamar hukumar Bali ta jihar Taraba
  • Wani mazaunin Maihula, Mallam Yakubu Bello, yace mutane sun wayi gari ne kawai sun ga bakin, kuma tuni matasa suka umarci su fice
  • Hukumar yan sandan jihar Taraba tace ba ta da masaniya kan shigar wasu baki garin Maihula

Taraba - Matasan garin Maihula dake ƙaramar hukumar Bali a jihar Taraba sun kori waru bakin mutane akalla 600, waɗan da suka shiga garin a cikin Tirela guda biyu.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa baƙin waɗan da suka haɗa da; mata da kananan yara, ana tsammanin daga jihar Zamfara suka fito.

Wani mazaunin garin Maihula, Mallam Yakubu Bello, ya shaida wa manema labarai cewa, sun gano bakin da suka shigo garin ne da sanyin safiyar ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Yan ta'addan ISWAP su kai wani mummunan hari mutane na tsaka da Sallah a jihar Yobe

Tirela cike da mutane
Tashin Hankali: Wasu bakin mutane akalla 600 sun shiga wata jiha a Arewa a Tirela biyu Hoto: vangaurdngr.com
Asali: UGC

Ya ƙara da cewa bakin sun dira garin a cikin Tireloli guda biyu, kuma mutane sun shiga tashin hankali domin babu wanda yasan manufar su ta zuwa garin.

Mallam Bello yace shigowar mutanen ya jawo matasa sun fusata, sun fara zanga-zangar ƙin amincewa da lamarin.

Meyasa mutane ke zargin baƙin?

Yace saboda karuwar lamarin sace-sacen mutane da ayyukan yan bindiga, mazauna garin musamman matasa sun tattaru kuma sun umarci baƙin su fice daga garin baki ɗaya.

"A halin yanzu da muke magana da ku, baƙin sun fara ficewa daga garin," inji shi.

Wani bincike ya tabbatar da cewa daruruwan mutanen jihar Zamfara yanzu haka suna Wurbo Daudu, Sodai, da kuma Boki, waɗan nan yankuna na kan hanyar Jalingo zuwa Bali.

Wane mataki hukumar yan sanda ta ɗauka?

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Yan bindiga sun bude wa mutane wuta a Zariya, sun kashe mutane

Kakakin rundunar yna sanda reshen jihar Taraba, DSP Usman Abdullahi, yace hukumarsu ba ta da masaniya kan shigar baƙi garin Maihula.

A wani labarin na daban kuma Wata fitacciyar jaruma a masana'antar Nollywood da aka tabbatar da mutuwarta ta tashi bayan awanni uku

Ɗiyar fitacciyar jarumar, Bisi Aisha, tace duk da cewa mahaifiyarta ta mutu, amma ta motsa wani bangare na jikinta bayan awa uku.

Aisha ta nuna godiyarta ga Allah da ya sake dawo musu da mahifiya, kuma ta gode wa masoya dake cigaba da musu addu'a.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel