Ministar Buhari ta magantu a kan zargin shirin korar ma’aikatan gwamnati

Ministar Buhari ta magantu a kan zargin shirin korar ma’aikatan gwamnati

  • Ministar kudi, Zainab Ahmed, ta yi watsi da rade-radin cewar gwamnatin tarayya na shirin sallamar ma'aikata
  • Misis Ahmed ta ce lokuta da dama shugaba Muhammadu Buhari ya sha nanata cewa babu ma'aikacin da za a sallama a gwamnatinsa
  • Sai dai, ta ce gwamnati za ta rage yawan kudaden da ake kashewa ta hanyar tabbatar da ganin cewa an hade hukumomin ta

Abuja - Ministar kudi, kasafin kudi da tsare-tsare na kasa, Zainab Ahmed ta ce babu wani shiri da ake yi na korar ma'aikatan gwamnati.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa ministar ta bayyana hakan ne a ranar Alhamis, 6 ga watan Janairu yayin wata hira a shirin barka da safiya na NTA.

Ministar Buhari ta magantu a kan zargin shirin korar ma’aikatan gwamnati
Ministar Buhari ta magantu a kan zargin shirin korar ma’aikatan gwamnati Hoto: Ministry of Finance, Budget and National Planning
Asali: Facebook

A hirar, Ahmed ta yi watsi da rade-radin cewa akwai wani shiri da gwamnatin tarayya ke yi na korar ma'aikata.

Kara karanta wannan

An samu sauyi: Bayan ayyana 'yan bindiga a matsayin 'yan ta'adda, Buhari ya bayyana yadda zai yake su

Ta ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sha bayyana cewar babu ma'aikacin da za a sallama daga aiki, rahoton Punch.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ahmed ta kuma bayyana cewa shugaban kasar ya kuma umurci ministoci da su biya albashin ma'aikatan gwamnati.

A ruwayar Punch, Ahmed ta ce gwamnati za ta dunga karfafawa mutane gwiwar barin aikin gwamnati ta hanyar basu abubuwan karfafa gwiwa.

Ta kara da cewar gwamnati za ta rage yawan kudaden da ake kashewa ta hanyar tabbatar da ganin cewa an hade hukumomin gwamnati.

Ta ce:

"Mai girma Shugaban kasa baya son sallamar ma'aikata. Wannan shine umarnin da ya bayar tun a farkon gwamnatinsa. Ya kuma umarce mu da mu biya albashi. Gwamnatin tarayya ba ta taba gaza biyan albashi ba kuma ya ce dole ne mu rika biyan fansho a kodayaushe. Ya sha nanata umarninsa kuma mun bi wadannan umarni."

Kara karanta wannan

Babbar magana: Ana kukan rashin aikin yi, gwamnatin Buhari za ta rage ma'aikata

Babbar magana: Ana kukan rashin aikin yi, gwamnatin Buhari za ta rage ma'aikata

A baya jaridar The Nation ta rahoto cewa ma'aikatan gwamnatin tarayya sun shiga tashin hankali a ranar Laraba yayin da gwamnatin tarayyar ta bayyana shirinta na rage yawan ma'aikatanta.

Rahoton ya ce tuni dai gwamnati ta fara shirin tanadarwa ma'aikatan da abun zai shafa wani kunshin sallama na musamman.

Sai dai kuma, ministar tace tsarin da gwamnati za ta bi wajen rage yawan ma'aikatan ba zai kasance daidai da rahoton Stephen Oronsaye ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel