Abun Mamaki: An gano fitacciyar Jarumar fina-finai a raye awanni bayan sanar da mutuwarta

Abun Mamaki: An gano fitacciyar Jarumar fina-finai a raye awanni bayan sanar da mutuwarta

  • Shahararriyar jaruma a masana'antar shirya fina-finai, Sidikat Odukanwi, ta rayu awanni kusan uku bayan sanar da cewa ta mutu
  • Ɗiyar fitacciyar jarumar, Bisi Aisha, tace duk da cewa mahaifiyarta ta mutu, amma ta motsa wani bangare na jikinta bayan awa uku
  • Aisha ta nuna godiyarta ga Allah da ya sake dawo musu da mahifiya, kuma ta gode wa masoya dake cigaba da musu addu'a

Bisi Aisha, ɗiyar shahararriyar jaruma a masana'antar Nollywood, Sidikat Odukanwi, wacce aka fi sani da Iyabo Oko, ta bayyana cewa mahaifiyarta na nan a raye.

Tun da farko dai Aisha ta fito ta bayyana wa mutane cewa Allah ya yi wa mahaifiyarta cika wa a jiya Laraba.

Sai dai awanni bayan haka, Aisha ta sake garzayawa shafinta na dandalin sada zumunta Instagram, inda tace duk da ta sanar da mutuwar mahaifiyarta, amma ta motsa yatsanta awanni uku bayan haka.

Kara karanta wannan

Sabon salo: Ministan Buhari ya fitar imel dinsa, ya roki 'yan Najeriya su fadi ra'ayinsu akan aikinsa

Iyabo Oko
Abun Mamaki: An gano fitacciyar Jarumar fina-finai a raye awanni bayan sanar da mutuwarta Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

A cikin wani sabon bidiyo, Aisha tace:

"Barkan ku da safiya, wannan ɗiyar Iyabo Oko ce. Iyabo Oko na nan da rai ba ta mutu ba, mahaifiyata na nan a raye."

Meyasa ta sanar da mutuwar tun farko?

Aisha ta kara da cewa ta sanar da mutuwar mahaifiyarta ne bayan yayanta ya tabbatar mata da haka a waya, amma bayan awanni kuma aka gano tana raye.

"Ni ce na sanar jiya bayan babban yayana ya kira ni a waya kuma ya tabbatar mun da mun rasa mahaifiyar mu, amma bayan awanni uku rayuwarta ta dawo."
"Dan haka muna kara godiya ga Allah. Idan kuka diba idanu na tun jiya nake kuka ina zubda hawaye amma yanzun kam mun gode Allah."
"Yanzun ran ta ya dawo, mahaifiyar mu na nan a raye. Iyabo Oko ba ta mutu ba, muna bukatar adu'arku. Muna godiya ga kowa da kowa."

Kara karanta wannan

Kannywood: Hafsat Shehu ta bayyana halin da ta shiga bayan rasuwar mijinta, Marigayi Ahmad S. Nuhu

A wani labarin na daban kuma Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Fitaccen Shehin Tijjaniyya a Najeriya ya riga mu gidan gaskiya

Daruruwan dubbannin mutane sun halarci Jana'izar Shehin Malamin, wanda ke da mabiya sosai kuma mutane ke matukar girmama shi.

Jami'an tsaro sun jigata sosai wajen kula da dandazom mutane da cunkoson abun hawa a Oniyangi, hanyar gidan Sarki, inda aka gudanar da sallar jana'izar mamacin.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel