Hana cin nama daga Arewa: Kungiyar masu safarar abinci da shanu sun mayar wa IPOB zazzafan martani

Hana cin nama daga Arewa: Kungiyar masu safarar abinci da shanu sun mayar wa IPOB zazzafan martani

  • Hadakar kungiyoyin dillalan shanu da kayan abinci na kasa ta ce barazanar da IPOB ta yi na hana cin naman arewa a kudu maso gabas shirme ne
  • Kungiyar ta bakin shugabanta Muhammad Tahir ta ce yankin na kudu ba zai iya rayuwa ko da kwana daya ne ba idan aka dena kai musu nama da abinci daga arewa
  • Tahir ya kara da cewa kungiyarsu tana goyon bayan zaman lafiya da cigaba da zama kasa daya al'umma daya amma idan ba haka IPOB ke so ba a shirye suke su

Gamayyar kungiyoyin masu sayar da kayan abinci da dillalan shanu a Najeriya, a ranar Laraba ta nuna cewa a shirye ta ke ta dakatar da hana kai kayan abinci da shanu yankin kudu maso gabashin Najeriya, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Bashin China: Ko yanzu muke bukatar bashi, za mu sake karbowa, Buhari

Kungiyar ta yi wannan furucin ne yayin mayar da martani kan sanarwar da kungiyar Indigenous People of Biafra (IPOB) masu son kafa kasar Biafra ta fitar na hana cin naman shanu daga arewa da kuma dena rera taken Najeriya.

Hana cin nama daga Arewa: Kungiyar masu safarar abinci da shanu sun mayar wa IPOB zazzafan martani
IPOB ta sha zazzafan martani bayan yin barazanar hana cin naman daga arewa a yankin kudu. Hoto: Daily Trust
Asali: Twitter

A hirar da aka yi da shi a BBC, Muhammad Tahir, shugaban kungiyar na kasa, ya bayyana umurnin na IPOB a matsayin farfaganda maras tushe, yana mai cewa, 'mun gaji da irin wannan barazanar.'

Muna son hadin kai amma duk abinda suka zaba a shirye muke, Tahir

Ya ce:

"Muna son Najeriya mai hadin kai - kasa daya al'umma daya; amma idan su (IPOB) suna ganin ba haka suke so ba, mu ma a cikin shiri muke.
"Ba abin cutarwa muke kai musu ba, a maimakon hakan, muna kai musu arziki ne zuwa yankinsu. Muna kai musu kayan abinci ne ba guba ba."

Kara karanta wannan

Ba za ta yiwu a tsaida Musulmi da Musulmi takara ba, sama da kasa za su hade inji CAN

Ya ce al'ummar da suke kudancin Najeriya ba za su iya rayuwa ba ko da na kwana daya ne ba idan an toshe hanyoyin kai abinci da nama daga arewa.

IPOB ta haramta cin naman shanun Fulani yayin bukukuwa a kudu maso gabashin Najeriya

Tunda farko, kun ji cewa haramtaciyyar kungiyar masu neman kafa kasar Biafra, IPOB, ta haramta cin naman shanun Fulani a yankin kudu maso gabashin Najeriya, Vanguard ta ruwaito.

IPOB, cikin sanarwar da ta fitar a ranar Litinin ta bakin mai magana da yawunta, Emma Powerful, ya ce dokar haramci zai fara aiki a watan Afrilu.

A cewar kungiyar, shanun kawai da ake kiwo a yankin ne za a rika amfani da su wuraren biki ko sha'ani a yankin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel