'Yan sanda sun ƙwato bindiga masu harbo jiragen yaƙi 109 a hannun 'yan ta'adda a Katsina

'Yan sanda sun ƙwato bindiga masu harbo jiragen yaƙi 109 a hannun 'yan ta'adda a Katsina

  • Rundunar 'yan sandan Najeriya reshen Jihar Katsina ta ce ta kwato bindiga masu harbo jiragen yaki har guda 109 daga hannun 'yan ta'adda cikin 2021
  • Mai magana da yawun rundunar, SP Gambo Isah ne ya bayyana hakan yayin zantawarsa da kamfanin dillancin labarai NAN a Katsina
  • Ya kuma lissafa wasu makaman daban da aka kamo da suka kunshi muggan bindigu, dabobi irinsu shanu, jaki da mutane da aka ceto daga hannun masu garkuwa ds

Katsina - Rundunar 'yan sanda a Jihar Katsina, ta ce ta kwato bindigu masu harbo jiragen sama na yaki guda 109 sannan ta kama mutane 999 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban a jihar a 2021.

SP Gambo Isah, Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan ne ya bayyana hakan yayin da ya ke zantawa da kamfanin dillancin labarai na kasa, NAN, a Katsina, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Tirkashi: 'Yan sanda sun kwace bindigogin harbo jiragen sama 109 daga 'yan bindigan Katsina

'Yan sanda sun ƙwato bindiga masu harbo jiragen yaƙi 109 a Katsina
'Yan sandan jihar Katsina sun kwato bindiga masu harbo jiragen yaki guda 109 hannun 'yan bindiga. Hoto: The Punch
Asali: UGC

Isa ya kuma ce rundunar ta kwato makamai da dama tare da bindigu a cikin shekarar da ta shude.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wasu daga cikin makaman da aka kwato

Ya lissafa wasu daga cikin makaman da aka kwato kamar haka; GPMG guda hudu, AK-47 guda 44, LAR guda daya, G3 guda daya, bindiga da aka kera a Najeriya guda 20 da kuma harsashi mai tsawon 7.62mm guda 689.

Dabobbi da aka kwato

Isa ya kuma ce an kwato dabobbi guda 1,243 da suka hada da shanu 867, tinkiya 352, akuya 24 da jaki guda daya.

Mutane da aka kama

Kakakin yan sandan ya cigaba da cewa:

"Wasu daga cikin wadanda aka kama sun hada da wadanda ake zargi da fashi da makami, garkuwa da mutane, satar shanu da sauransu. Cikin wadanda ake zargi da fashi 157 da aka kama, an gurfanar da 145 a kotu yayin da ana bincike kan saura 12.

Kara karanta wannan

2023: Ƙungiyar arewa ta bayyana sanata daga kudu da ta ke son ya gaji Buhari

"Kazalika, an kama wadanda ake zargi da garkuwa su 65, an kai 63 kotu yayin da ake bincike a kan biyu.
"Mun yi nasarar kama wadanda ake zargi da satar shanu su 244, an gurfanar da 230 cikinsu a kotu yayin da saura 14 ana bincike a kansu.
"A cikin shekarar, an bindige wasu da ake zargi yan bindiga ne su 38 yayin da yan sanda biyar suka riga mu gidan gaskiya."

Ya kara da cewa an kama mutane 246 kan cin zarafi yayin da aka ceto mutum 63 daga hannun masu safarar mutane kuma an tura su hannun hukumar NAPTIP ta Kano.

'Yan sanda sun kama wasu mutane 2 suka kashe malamin addinin suka sace kuɗinsa bayan ya basu masauki

A wani rahoton, 'yan sandan Jihar Legas, sun kama wasu mutane biyu, Farouk Mohammed da Jamiu Kasali da ake zargi da kashe wani Babatunde Dada, fasto na cocin Redeemed Christian Church of God (RCCG) a FESTAC Legas.

Kara karanta wannan

‘Yan bindiga sun farmaki gidan jami’in dan sandan IRT, sun kashe mutum 1 a Zaria

Kwamishinan yan sandan Jihar Legas, Hakeem Odumosu, ya tabbatar da kama Mohammed da aka bi sahunsa zuwa Ilorin, Jihar Kwara, shi kuma abokin laifinsa, Kasali, aka kama shi a FESTAC, Legas, Guardian ta ruwaito.

https://hausa.legit.ng/news/1450475-yan-sanda-sun-kama-wani-da-ake-zargi-da-kashe-malamin-addini/

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel