Direban mota ya daba wa matarsa wuka har Lahira bayan ya sake ta a Adamawa

Direban mota ya daba wa matarsa wuka har Lahira bayan ya sake ta a Adamawa

  • Wani direba ya hallaka matarsa ta hanyar daba mata wuka a kirji a garin Lande, yankin karamar hukumar Gambi, jihar Adamawa
  • Lamarin ya auku a ranar 1 ga watan Janairu na sabuwar shekara, bayan matar ta fusata mijin har ta kai ga ya sake ta
  • Kakakin hukumar yan sandan jihar Adamawa yace kwamishina ya yi kira ga mutane su daina ɗaukar doka a hannun su

Adamawa - Wani mutumi ɗan kimanin shekara 57, Muhammad Alpha, ya daɓa wa matarsa, Hamsatu, wuka har tace ga garin ku nan a ranar farko ta sabuwar shekara.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne a garin Lande dake yankin karamar hukumar Gambi a jihar Adamawa.

Kakakin rundunar yan sanda reshen jihar, DSP Sulaiman Nguroje, shi ne ya tabatar da haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi a Yola.

Kara karanta wannan

Nasara daga Allah: Sojoji sun tarwatsa shugabannin 'yan bindiga a Zamfara

jihar Adamawa
Direban mota ya daba wa matarsa wuka har Lahira bayan ya sake ta a Adamawa Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Meyasa ya kashe matarsa?

Yace wanda ake zargi, ɗan kasuwa mai aikin tuƙin mota, ya caka wa marigayya matarsa, Hamsatu Muhammad, yar shekara 40 wuka bayan wata ƙaramar taƙaddama ta haɗa su.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ƙara da cewa taƙaddamar da ta shiga tsakanin su ce ta yi sanadin mutuwar auren su, wanda suka shafe shakaru sama da 20 a tare da juna.

Kakakin yan sandan yace a ranar 1 ga watan Janairu, 2022, hukumar yan sanda ta damke direban bisa zargin hallaka matarsa Hamsatu, kamar yadda Punch ta rahoto.

Me binciken yan sanda ya tabbatar?

A cewar kakakin yan sandan bayanan da suka samu na farko ya nuna cewa bayan rabuwar ma'auratan, matar ta koma wani gida kusa da gidan tsohon mijinta.

Yace:

"A kokarinta na gyara sabon ɗakinta, matar taje gidan tsohon mijinta ta ciro kofa domin gyara sabon wurin zamanta."

Kara karanta wannan

An kama masu garkuwa da mutane yayin da suke jiran kudin fansar wadanda suka sace a Katsina

"Abin da ta yi ne ya fusata wanda ake zargin, shi ne yasa ya yi amfani da wuka ya daba wa matarsa kuma uwar 'ya'yansa 8 a kirji."
"Sakamakon haka ta samu mummunan rauni, mutane suka yi gaggawar kaita asibiti ma fi kusa, inda aka tabbatar da ta mutu."

Kwamishinan yan sanda na jihar, Mohammed Barde, ya bada umarnin gudanar da bincike kan lamarin, kuma ya roki mutane su daina ɗaukar doka a hannun su.

A wani labarin na daban kuma Yan bindiga sun yi awon gaba da tsohon dan takarar gwamna a jihar Arewa

Yan bindiga sun kutsa har cikin gidan wani jigon PDP a jihar Filato dake arewa ta tsakiya kuma tsohon ɗan takarar gwamna, sun yi awon gaba da shi

Wani abokinsa ya tabbatar da cewa maharan sun kira wayar ɗaya daga cikin yayansa, sun nemi a haɗo musu miliyoyi kudin fansa da wuri-wuri.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: Jami'an NSCDC sun gano gawarwakin matasa uku a Kogin jihar Benuwai

Asali: Legit.ng

Online view pixel