Abun bakin ciki: ‘Yan gida daya su biyu sun nitse a ruwa a jajiberin sabuwar shekara

Abun bakin ciki: ‘Yan gida daya su biyu sun nitse a ruwa a jajiberin sabuwar shekara

  • Wani abun bakin ciki ya afku a jajiberin sabuwar shekara lokacin da wasu yara biyu 'yan gida daya suka hadu da ajalinsu a Kogin Asa da ke Ilorin, babbar birnin jihar Kwara
  • Yaran sun nitse ne a cikin ruwan yayin da suke wanka kamar yadda suka saba tare da abokan wasansu
  • Jami’an hukumar kashe gobara ta jihar Kwara sun tsamo gawawwakin yaran daga kogin

Kwara - Wasu matasa biyu yan gida daya, Damilare mai shekaru 12 da Kamaldeen mai shekaru 14 sun nitse a kogin Asa a yayin da suke wanka a ranar Juma’a, 31 ga watan Disamba.

Jami’an hukumar kashe gobara ta jihar Kwara sun tsamo gawawwakin yaran daga kogin, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

‘Yan sanda sun kai samame sansanin ‘yan bindiga a Kaduna, sun ceto mutum 9

Abun bakin ciki: ‘Yan gida daya su biyu sun nitse a ruwa a jajiberin sabuwar shekara
Abun bakin ciki: ‘Yan gida daya su biyu sun nitse a ruwa a jajiberin sabuwar shekara Hoto: Channels TV
Asali: UGC

Lamarin wanda ya faru a hanyar unguwar Mubo yankin kogin, Maraba, Ilorin, sun bar iyalai da mazauna yankin a cikin dimuwa.

Kakakin hukumar kashe gobara ta jihar Kwara, Hassan Adekunle, ya tabbatar da lamarin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa:

“Mummunan lamarin ya afku ne da karfe 4:36 na rana lokacin da wani Alhaji Eleja ya sammaci hukumar zuwa wajen da abun ya wakana.
“Sai dai, abun bakin ciki an samo yaran biyu a mace daga kogin.
“Wadanda abun ya cika da su sun fito daga gidan Ile-lalu, yankin Sabo-Line, Ilorin inda suka je yin wanka tare da abokan wasansu.”

Ya ce daraktan hukumar kashe gobara ta jihar Kwara, Prince Falade John Olumiyiwa, ya bukaci jama’a, musamman iyaye da malamai da su sanya idanu kan duk wani motsi na yaransu, musamman a wannan lokaci na hutu don guje ma faruwar irin haka a gaba.

Kara karanta wannan

Hatsarin kwale-kwale: Fasto da wasu mutane shida sun mutu a jajiberin sabuwar shekara

A ruwayar Channels TV, majiyoyi sun ce yaran tare da abokan wasansu sun tafi bakin kogi ne domin yin nishadi kamar yadda suka saba kafin faruwar lamarin.

Hatsarin kwale-kwale: Fasto da wasu mutane shida sun mutu a jajiberin sabuwar shekara

A wani labarin, al'umman garin Ogbinbiri da ke karamar hukumar Ijaw ta kudu a jihar Bayelsa sun shiga alhini a jajiberin sabuwar shekara sakamakon mutuwar wani fasto da wasu mutane shida.

A cewar idon shaida, lamarin ya afku ne lokacin da wasu kwale-kwale biyu suka yi karo, inda suka kife a ranar Laraba, 31 ga watan Disamba.

Marigayin mai shekaru 39 wanda aka ambata da suna Fasto Salvation Degemy, ya kasance shugaban cocin Supernatural Church of God da ke garin, jaridar The Sun ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel