Kukah: Lokacin zaɓe ne kaɗai ƴan Najeriya suke tuna addini banda lokacin sata

Kukah: Lokacin zaɓe ne kaɗai ƴan Najeriya suke tuna addini banda lokacin sata

  • Rabaran Matthew Kukah, Bishop din Katolika na shiyyar Sokoto ya ce lokacin zabe ne kadai ake tuna addini a Najeriya
  • A cewarsa duk masu kallon matsalar tsaro a matsayin matsalar addini ba sa fada wa ‘yan Najeriya gaskiya, don haka a daina yaudarar juna
  • Ya yi wannan bayanin ne a ranar Juma’a yayin tattaunawa da manema labarai a Sokoto inda yace ya kamata a falka kafin kasar ta lalace gaba daya

Jihar Sokoto - Matthew Hassan Kukah, bishop din cocin Katolikan shiyyar Sokoto ya ce ‘yan Najeriya su na tuna addini ne kadai lokacin zabe, The Cable ta ruwaito.

A cewarsa duk wadanda su ke daukar matsalar tsaro a matsayin matsalar addini su na yaudarar ‘yan Najeriya.

Kukah: Lokacin zaɓe ne kaɗai ƴan Najeriya suke tuna addini banda lokacin sata
Bishop Kukah ya ce lokacin zaɓe ne kaɗai ƴan Najeriya suke tuna addini amma banda lokacin sata. Hoto: The Cable
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa rashin tsaro zai zo karshe ne idan ‘yan kasa sun daina ci gaba da yaudarar junayensu.

Kukah ya ce mu hada kawunanmu

Kukah ya bayyana hakan ne bisa ruwayar The Cable a ranar Juma’a yayin tattaunawa da manema labarai a Sokoto.

“Matsawar ba mu daina yaudarar kawunanmu ba, Najeriya ba za ta taba samun cikakken tsaro ba kuma za a ci gaba da samun matsaloli har nan gaba,” a cewarsa.

Ya kara da cewa:

“A Najeriya ne kadai za ka ji musulmi ko kirista yana tuna addinin shugaban kasa idan zabe yazo, amma batun sata da rashawa duk daya ake.
“Ban ce kirista ya zama shugaban kasan Najeriya ba amma muna bukatar Shugaban da zai kula da kasar nan. Muna bukatar hadin kan Najeriya don babu wanda ya fi wani muhimmanci."

A hada kai da shugabanni wurin kawo karshen matsalolin tsaro

A cewarsa lokaci ya yi da kowa zai mayar da hankali akan matsalolin Najeriya, da an hada kai don kawo karshen duk damuwar da ta addabi kowa.

Ya bukaci ‘yan Najeriya su kasance masu zaman lafiya da juna kuma su ci gaba da taimaka wa gwamnati wurin yaki da rashin tsaro.

Kukah: Duk da yawan sukar da na ke yi wa gwamnatinsa, Buhari bai dena daukan waya na ba

A wani labarin, Rabaran Matthew Hassan Kukah, Bishop din cocin Katolika da ke shiyyar Sokoto, ya ce duk da caccakar gwamnatin shugaban kasa Buhari, shugaban bai daina daga wayarsa ba, Daily Trust ta ruwaito.

Faston wanda yana daya daga cikin manyan masu caccakar gwamnati wanda ya yi hakan sau dayawa, ya taba zargin Buhari da rashin adalci ta hanyar fifita na kusa da shi.

Yayin tattaunawa da manema labarai a ofishin cocin Katolika ta St Bakhita a ranar Juma’a, Kukah ya ce su na ci gaba da zumunci da Buhari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel