Arewa TikTok: Bayan lakaɗawa 'Suddenly' duka har gida, ƴan sandan Kano sun shiga tsakani

Arewa TikTok: Bayan lakaɗawa 'Suddenly' duka har gida, ƴan sandan Kano sun shiga tsakani

  • Rikicin wasu abokan hamayyar TikTok na arewacin Najeriya, Aisha Zaki da Suddenly wanda ko wacce ta tara mabiya a bayanta ya janyo gagarumin tashin hankali
  • Bangaren Aisha Zaki sun bi Suddenly har gida inda su ka taru su ka yi mata dukan tsiya yayin da bidiyonsu su na aika-aikar ya yadu a kafafen sada zumunta
  • Aisha Zaki ta saki bidiyo tana yaba wa yaranta akan aika-aikar da su ka yi yayin da Suddenly ta saki nata bidiyon ta ta bayyana cewa bata tsoro

Jihar Kano - Rikicin TikTok ya janyo wasu abokan hamayya biyu na arewacin Najeriya, Aisha Zaki da Suddenly sun fara ba hammata iska, The Cable ta ruwaito.

Su biyun sun fara tara mabiya ta kafar wanda hakan ya janyo gagarumin tashin hankali har mabiyan daya su ka titsiye daya tare da zane ta har gida.

Kara karanta wannan

Magidanci ɗan shekaru 80 ya kashe matarsa don ta fasa kwanciyar aure da shi bayan ya sha maganin ƙarfin maza

Arewa TikTok: Bayan lakaɗawa 'Suddenly' duka har gida, ƴan sandan Kano sun shiga tsakani
Bayan lakaɗawa 'Suddenly' duka har gida, ƴan sandan Kano sun shiga tsakani. Hoto: Suddenly
Asali: Instagram

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

BBC Pidgin ta bayyana yadda mabiyan Aisha Zaki su ka bi Suddenly har gida su ka dinga jibgar ta sannan su ka wallafa bidiyon dukan nata a kafar sada zumunta.

Aisha Zaki ta yaba wa yaranta

A bangaren Aisha Zaki, ta wallafa wani bidiyo a TikTok inda ta yaba wa yaranta akan dukan abokiyar hamayyarta da su ka yi inda ta kara da cewa ba karshen rigimar kenan ba.

A bangaren Suddenly ta yi wani bidiyo tana cewa ba ta tsoron kowa.

Tushen lamarin

Bala Bashir, wani dan TikTok ya ce rikicin da ke tsakanin Aisha Zaki da Suddenly kawai na yakin tantance wanda ya fi wani zama sananne a TikTok ne.

A cewarsa:

“Da farko ko wacce ta fara gadara ne akan abinda ta mallaka daga bisani su ka fara zagin juna saboda Aisha Zaki a Saudi Arabia ta ke zama kuma a can take aiki."

Kara karanta wannan

Bidiyon yadda wasu suka ba hammata iska a yayin da ake tsaka da wa’azi a coci

Yayin da Bala ya yi kira ga jami’an tsaro akan su shiga cikin lamarin, Abdullahi Haruna Kiyawa, Kakakin rundunar ‘yan sandan Kano ya ce yanzu haka su na bincike akan rikicin.

Kano: Ƴan Sanda Sun Kama Sojan Bogi, Zailani-Ibrahim Da Ya Ƙware Wurin Tatsar Masu Keke Napep

A wani labarin daban, rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta samu nasarar damkar sojan bogi wanda ya kware wurin damfarar masu Napep, The Nation ta ruwaito.

Jami’in hulda da jama’an rundunar, DSP Abdullahi Kiyawa ne ya tabbatar da kamen a wata takarda wacce ya ba manema labarai ranar Talata a Kano.

A cewarsa, wanda ake zargin, Abubakar Zailani-Ibrahim, mai shekaru 27 ya gabatar wa da ‘yan sandan ofishin Rijiyar Zaki kansa a matsayin soja kuma ya je da wani mai Napep.

Asali: Legit.ng

Online view pixel