Bidiyon Sarkin Bauchi yana rera wakar yabo yayin da ya karbi bakuncin Kiristoci a fadarsa

Bidiyon Sarkin Bauchi yana rera wakar yabo yayin da ya karbi bakuncin Kiristoci a fadarsa

  • Jama'a sun tofa albarkacin bakunansu yayin da Sarkin Bauchi ya karbi bakuncin wasu mabiya addinin Kiristanci a fadarsa a yayin bikin kirsimeti
  • A cikin wani bidiyo da yayi fice, an gano Basaraken wanda yake Musulmi yana rera wakar dawowar Annabi Isah tare da bakin nasa
  • Sai dai hakan ya birge mutane da dama inda suka ce addini ba komai bane face soyayyar juna

Bauchi - Mai martaba sarkin Bauchi ya karbi bakuncin wasu mabiya addinin Kiristanci a fadarsa a yayin bikin kirsimeti.

A yayin taron, sarkin wanda ya kasance Musulmi, ya yi wa kiristocin jawabi a kan gudanar da rayuwa mai kyau wanda za a yi koyi da shi.

Shafin Linda Ikeji ya ruwaito cewa a yayin taron, basaraken wanda ke zaune a kan kujerarsa ta mulki ya kuma rera wakar 'Annabi Isah na nan dawowa ba da jimawa ba'.

Bidiyo: Sarkin Bauchi ya karbi bakuncin Kiristoci a fadarsa, ya fada masu cewa Annabi Isa na nan dawowa
Bidiyo: Sarkin Bauchi ya karbi bakuncin Kiristoci a fadarsa, ya fada masu cewa Annabi Isa na nan dawowa Hoto: @lindaikejiblogofficial
Asali: Instagram

Yana fara wakar sai jazaba ta kama kiristocin da ke wajen inda suka tashi suka taya shi rera wakar tare da tafa hannu.

Kalli bidiyon a kasa:

Wannan al'amari birge yan Najeriya da dama ganin cewa basaraken da kiristocin sun yi tarayya cikin aminci da kaunar juna duk da banbancin addini da ke tsakaninsu.

Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin martanin jama'a kan bidiyon a kasa:

aijay_da_realtor ya yi martani:

"Kauna ita ce addini ta gaskiya."

ekemezie_amaka ta ce:

"❤️❤️❤️a bari kauna tayi jagoranci"

alaya_fatty ta ce:

"Mu Musulmai mun yarda da dawowar Annabi Isa, wannan ba labari bane. Yana cikin Al-Qur'ani amma abun da zai dawo yi ya banbanta da abun da ku kuka yarda da shi. Ban ga wani abu ba a nan, wannan shi ake kira juriyar addini. Idan za mu dunga hakuri da junanmu Najeriya za ta sake inganta."

arewa_arise ya ce:

"@officialjogarba yana rubuce a Al-Qur'ani"

Bidiyon yadda wasu suka ba hammata iska a yayin da ake tsaka da wa’azi a coci

A gefe guda, mun kawo cewa an sha yar dirama a cocin Olivet Baptist da ke Chattanooga, Tennessee a ranar Lahadi, 26 ga watan Disamaba, 2021, lokacin da mambobin cocin biyu suka ba hammata iska yayin da faston ke wa’azi.

An gano wani dan cocin a bidiyo yana tunkarar wani da ke zaune hankali kwance yana sauraron sakon da faston ke isarwa.

Kawai sai mutumin da ba a bayyana kowanene ba ya kaiwa na zaunen naushi, lamarin da yasa shima ya tashi ya far masa inda suka bai wa hammata iska.

Asali: Legit.ng

Online view pixel