Bai zo a littafi mai tsarki ba: Kirista ta caccaki masu bikin Kirsimeti

Bai zo a littafi mai tsarki ba: Kirista ta caccaki masu bikin Kirsimeti

  • Wata mai wa'azi ta haddasa cece-kuce a shafukan sadarwa bayan ta yi wa'azi kan bikin Kirsimeti
  • Matar ta bayyana cewa littafi mai tsarki (injila) bai goyi bayan bikin ba kuma babu wani shaida da ke nuna cewa an haifi Annabi Isah a wannan rana
  • 'Yan Najeriya a yanar gizo basu gamsu da ikirarinta ba yayin da suke mamakin dalilinta na kokarin tursasa mutane su yarda da abun da ita tayi imani a kai

Wani bidiyo da shafin @instablog9ja ya wallafa a Instagram ya nuno lokacin da wata mai wa'azi ta baje kolinta na yin wa'azi a wajen na'urar ATM bayan wani ya taya ta murnar Kirsimeti.

Da take bayani kan addininta, matar ta bayyana cewa babu wani waje a littafi mai tsarki (Injila) da aka yi bikin Kirsimeti, inda ta bayyana hakan a matsayin kafirci.

Kara karanta wannan

Ba zata sabu ba: Iyayen amarya sun fasa aurar da 'yarsu bayan ganin gidan da ango zai aje ta

Bai zo a littafi mai tsarki ba: Kirista ta caccaki masu bikin Kirsimeti
Bai zo a littafi mai tsarki ba: Kirista ta caccaki masu bikin Kirsimeti Hoto: @instablog9ja
Asali: Instagram

Littafin Injila bai goyi bayan Kirsimeti ba

Ta ci gaba da bayyana cewa bikin ya bai wa mutane da dama kafar yin duk wasu abubuwan shaidanci.

Mai wa'azin ta bayyana cewa babu wani waje a littafi mai tsarki inda aka rubuta cewa an haifi Yesu Almasihu a ranar Kirsimeti.

A lokacin da mutanen da ke kan layin suka bayyana rashin yardarsu, sai malamar ta tsaya kan bakarta, cewa babu wani abu na Allah a tattare da bikin.

Kalli bidiyon a kasa:

Ga martanin jama'a a kasa:

mcmakopolo1 ya ce:

"An shirya nadar bidiyon ne amma dai ta iya shiri sosai."

just.chelsea_ ya ce:

"Ba dole bane yi wa mutum barka da Kirsimeti."

kleopatrus ta ce:

"Mai wa'azin Kiristanci na sanya Kimar? Ku kara wayar mun da kai dan Allah."

Kara karanta wannan

Bakon lamari: Bidiyon dan sanda na raba wa matafiya buhunan shinkafa ya jawo cece-kuce

hardewunmii__ ta ce:

"Abu kadan ke fusata wanda bai da kayan Kirsimeti faa."

Wani mutum ya mutu wurin gasar cin abinci yayin bikin Kirsimeti a Uganda

A wani labarin, wani mutum mai shekaru 56 mai suna Sentekola Gad, ya shake kansa da abinci yayin gasar cin abinci a ranar Kirsimeti a kasar Uganda LIB ta ruwaito.

Mai magana da yawun yan sanda, Fred Enanga, ya ce Sentekola ya shiga gasar cin abinci ne da wani Salvan a ya shirya a Kihiri, a yankin Kanungu.

A yayin da ya ke yi wa manema labarai jawabi a ranar Litinin, Enanga ya ce:

"Wanda abin ya faru da shi ya shake kansa ne a abinci kuma aka dauke shi aka kai cibiyar lafiya ta Kihihi inda aka tabbatar abincin ne ya kashe shi."

Asali: Legit.ng

Online view pixel