Tashin Hankali: Wani mutumi ya mutu a cikin tankin Tankar man fetur a Kano

Tashin Hankali: Wani mutumi ya mutu a cikin tankin Tankar man fetur a Kano

  • Wani direban mota, Dahiru Aliyu, ya rasa rayuwarsa ya yin da ya shiga tankin Tankar dakon man fetur a jihar Kano
  • Hukumar kwana-kwana ta jihar ta bayyana cewa jami'ai sun samu rahoton faruwar lamarin kuma sun yi gaggawar kai ɗauki
  • Rahoto ya nuna cewa mutumin ya shiga tankar ne da wata yar kwantena domin share mai da ya zuba, amma ya gamu da ajalinsa

Kano - Hukumar kwana-kwana ta jihar Kano ta tabbatar da mutuwar wani mutumi direban tanka ɗan shekara 45, Ɗahiru Aliyu, a depot ɗin NNPC dake Hotoro.

Vanguard tace hukumar ta tabbatar da mutuwar direban ne a wata sanarwa da kakakinta, Alhaji Saminu Abdullahi, ya fitar ranar Talata.

Tanker
Tashin Hankali: Wani mutumi ya mutu a cikin tankin Tankar man fetur a Kano Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Yace:

"Lamarin ya faru ne ranar Litinin da safe. Mun samu kiran gaggawa daga wani Shu’aibu Muhammad da misalin ƙarfe 10:59 na safe, kuma nan take muka tura jami'an ceto wurin."

Kara karanta wannan

Jami'an hukumar NSCDC guda 7 sun mutu a bakin aiki a jihar Neja

Me ya yi sanadin mutuwar direban?

Ya ƙara da cewa Aliyu ya shiga ɗaya daga cikin tankin da wani mazubi domin kwashe man fetur ɗin da ya zube.

A yayin haka ne direban ya rasa ingantacciyar iskar shaka kuma hakan ya yi sanadin mutuwarsa a cikin tankin, kamar yadda Daily Nigerian ta rahoto.

Bugu da ƙari, Mista Abdullahi ya bayyana cewa tankar dakon man fetur ɗin da ta yi ajalin mutumin na da lambar rijista DKD 411 XF.

A wani labarin na daban kuma gwamnan jihar Katsina dake makwaftaka da Kano yace gwamnatinsa zata taimaka wa mutane sun mallaki bindigu domin kare kansu

Masari yace abun takaicin shine yan ta'adda na da hanyoyin samun bindigu, da sauran makamai, amma mutanen kirki dake son kare kansu ba su da hanyoyin mallaka.

Kara karanta wannan

Dr Isa Pantami ya yi kuka kan yadda matasa sukayi wawaso a kantin da yayi gobara a Abuja

Gwamnan ya bayyana cewa gwamnatin jiha zata tallafa wa mutane, waɗan da ke son mallakan makamai domin taimakawa wajen dawo da zaman lafiya a faɗin jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel