Zamu taimaki mutane su mallaki bindigu domin kare kansu daga sharrin yan bindiga, Gwamna

Zamu taimaki mutane su mallaki bindigu domin kare kansu daga sharrin yan bindiga, Gwamna

  • Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya bayyana shirin gwamnatinsa na taimaka wa mutane su mallaki makamai don kare kansu
  • Masari yace abun takaicin shine yan ta'adda na da hanyoyin samun bindigu, amma mutanen kirki dake son kare kansu ba su da hanyoyi
  • Yace gwamnati na son kowane mutum ya tsaya ya kare yankin da ya fito da al'ummarsa

Katsina - Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Ƙatsina ya yi kira ga mutanen dake zaune a jihar Katsina su mallaki makamai domin kare kansu daga harin yan bindiga.

Rahoton BBC Hausa ya bayyana cewa yayin da yake amsa tambayoyin yan jarida, Masari yace adadin jami'an tsaro a jihar Katsina be kai 3,000 ba.

Gwamnan ya bayyana cewa gwamnatin jiha zata tallafa wa mutane, waɗan da ke son mallakan makamai domin taimakawa wajen dawo da zaman lafiya.

Gwamnan Katsina, Aminu Masari
Zamu taimaki mutane su mallaki bindigu domin kare kansu daga sharrin yan bindiga, Gwamna Hoto: ripplesnigeria.com
Asali: UGC

A jawabinsa yace:

"Tsaro ya rataya a kan kowa, abin da muke son mutane su sani shine a Katsina ba mu da yan sanda 3,000. Saboda haka muna kira duk me son kare kansa da iyalansa ya nemi makami."
"Addinin musulunci ya amince mutum ya kare kansa, dukiyarsa da kuma iyalansa. Idan mutum ya mutu wajen kare kansa ya yi shahada."
"Abin takaicin shine yan bindiga na da hanyoyin samun bindigu amma mutanen kirki ba su da hanyoyin mallakar bindigun da za su yi amfani wajen kare kansu."

Zamu taimaka wa mutane - Masari

Gwamnan yace gwamnati zata taimaki duk wani mutumi dake son mallakar makami domin dakatar da ayyukan yan bindiga.

"Zamu taimaki duk masu son mallakar makamai, saboda akwai bukatar mutanen jihar Katsina su tallafa wa hukumomin tsaro."

Shin Katsina na goyon bayan yan Bijilanti?

Gwamnan ya kuma soki ayyukan da yan bijilanti ke aiwatarwa domin suna barin yankunan su zuwa wasu garuruwan.

A cewar Masari, gwamnati ta fi bukatar kowane mutum ya tsaya ya kare yankin da ya taso da al'ummarsa, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

A wani labarin na daban kuma Yan bindiga sun hallaka Basarake da wasu mutane a sabon harin jihar Zamfara

Wasu miyagun yan bindiga sun kashe basarake a wani sabon hari da suka kai yankin masarautar Bungudu, jihar Zamfara.

Mazauna kauyen Gada sun bayyana cewa maharan sun cinna wuta a motocin masarauta da kuma kayan abincin da suka taras.

Asali: Legit.ng

Online view pixel