Masari ya sanar da ranar da za a dawo da sabis baki ɗaya a Katsina

Masari ya sanar da ranar da za a dawo da sabis baki ɗaya a Katsina

  • Gwamna Aminu Bello Masari na Jihar Katsina ya ce za a dawo da sabis a dukkan yankunan jihar kafin Janairun 2022
  • Masari ya bayyana hakan ne a ranar Talata 28 ga watan Disamba yayin da ya ke zantawa da manema labarai a Katsina
  • Gwamna Masari ya kuma shawarci mutanen jihar su cigaba da bawa hukumomin tsaro hadin kai musamman basu bayanai masu amfani

Jihar Katsina - Gwamnatin Jihar Katsina ta ce za ta dawo da sabis na sadarwa a sauran kananan hukumomi bakwai da aka toshe hanyoyin sadarwan kafin Janairun 2022, The Punch ta ruwaito.

Gwamnan, wanda ya bayyana hakan yayin hira da manema labarai a ranar Talata a Katsina,ya bukaci mutanen jihar su yi iya kokarinsu don ganin sun kare kansu daga hare-haren yan bindigan.

Masari ya sanar da ranar da za a dawo da sabis baki daya a Katsina
Masari ya ce za a dawo da sabbis a dukkan yankunan Katsina kafin Janairun 2022. Hoto: The Punch
Asali: Twitter

Kamfanin Dillancin Nigeria, NAN, ta rahoto cewa gwamnatin jihar a baya-bayan nan ta dawo da sabis a 10 cikin kananan hukumomi 17 na jihar da ke fama da hare-haren yan bindiga.

Kara karanta wannan

Dattawan Zamfara sun zargi hukumomin tsaro da sakin 'yan bindigan da suka kama

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya yaba wa kokarin hukumomin tsaro, musamman kungiyoyin sa-kai da yan banga da ke yaki da yan bindiga.

Premium Times ta rahoto Masari ya bayyana cewa yan bangan su kan yi tafiya daga gari zuwa gari domin basu kariya daga harin yan bindigan.

Masari ya shawarci al'umma su tashi su kare kansu

Gwamnan ya shawarci al'umma su tashi su kare kansu sannan su bawa hukumomin tsaro hadin kai da suke bukata musamman ta hanyar basu bayanai masu amfani.

Gwamnan ya bukaci mutanen garuruwan su taimakawa yan banga da makamai da suke bukata saboda su samu ikon kare kansu idan an kawo musu hari.

Hakazalika, Masari ya ce ya zama dole a kawo karshen yan bindigan da ke adabar yankunan arewa kafin shekarar 2023 kafin wa'adin gwamnatocin ya zo karshe.

Sokoto: 'Yan ta'adda sun naɗa sabbin hakimai da dagatai, sun bude kasuwanni da gwamnati ta rufe

Kara karanta wannan

Karya ne yan bindiga basu kai hari mahaifar sakataren Buhari a Adamawa ba – Yan sanda

A wani labarin, yan ta'adda da aka fi sani da yan bindiga sun nada wasu mambobinsu a matsayin dagatai a wasu kauyuka a karamar hukumar Sabon Birni a jihar Sokoto.

A cewar wata jaridar intanet ta Sokoto, Daily Star, kasurgumin shugaban yan bindiga, Turji ne ya nada sabbin dagatan.

Rahoton ya ce an fara kiran yan ta'addan su kira yan kauyen Gangara su hallarci taro a kauyen Suturu a ranar Alhamis inda aka sanar da sauke tsaffin dagatan sannan suka nada mambobinsu a matsayin sabbin shugabanni.

Asali: Legit.ng

Online view pixel