2022: Jerin yankunan da za su fuskanci rashin wutar lantarki a Najeriya

2022: Jerin yankunan da za su fuskanci rashin wutar lantarki a Najeriya

  • Gidaje a Najeriya sun shirya shiga sabuwar shekara amma kuma babu wutar lantarki domin kuwa yawan wutar da Najeriya ke samarwa ta ragu
  • Har zuwa yau, mafi yawan wutar lantarkin da kasar nan ke iya samarwa kamar yadda Nigerian Electricity System Operators shi ne 5801.6MW
  • Sai dai 'yan Najeriya na bukatar sama da 19,000MW, TCN na rarrabe wa kamfanoni 12 wutar inda suke samar wa jihohi Najeriya 36 wutar lantarkin

Gidaje masu yawa na Najeriya ya zama dole su gyara janaretocinsu yayin da suke shirin shiga sabuwar shekara saboda yawan wutar da kasar ke samarwa ta ragu da kashi talatin.

A ranar Laraba, 29 ga watan Disamba, Kamfanin samar da wutar lantarki, TCN, ya nuna cewa wutar lantarkin da kasar nan ke samarwa ta ragu zuwa 3,535.02MW, mafi karanci a cikin kwanakin nan.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Jigawa ta amince da hukuncin kisa kan masu haike wa yara

2022: Jerin yankunan da za su fuskanci rashin wutar lantarki a Najeriya
2022: Jerin yankunan da za su fuskanci rashin wutar lantarki a Najeriya. Hoto daga TCN
Asali: Getty Images

Wannan al'amarin kuwa ya tada hankalin kamfanin samar wutar lantarkin na Najeriya wanda ke tura wutar ga kamfanonin rarrabe wutar.

Kamar yadda bayanan TCN suka nuna, Najeriya ta na bukatar 19,000MW na wutar lantarki, wanda hakan ke nufin dloe ta samu hanyar rufe gibin da aka samu inda ta rarrabe wutar yadda ya sauwaka.

Dalla-dalla yadda TCN za ta rarrabe wutar

Daga cikin 3,535.02MW, Ikeja Disco za ta dinga samun 593.35MW domin bai wa sassan jihar Legas wuta da ya hada da Abule Egba, Akowonj, Ikeja, Ikorodu, Oshodi da Shomulu.

Za a bai wa Ibadan Electricity Distribution 448.57MW. Wannan kamfanin ai bai wa jihohin Oyo, Ogun, Osun, Kwara da wasu sassan jihohin Niger, Ekiti da Kogi wutar lantarki.

Kamfanin rarrabe wutar lantarki na Eko ne a biye inda zai samu 461.79MW inda zai dinga samar wa sassan jihar Legas da ya hada da Ojo, Festac, Ijora, Mushin, Apapa, Lekki, Lagos Island da kuma sassan jihar Ogun wuta.

Kara karanta wannan

Mummunar gobara ta yi kaca-kaca da wasu kasuwanni biyu a jihar Sokoto, ta kone shaguna

Kamfanonin 3 na karshe

Daga tsarin, Jihohin Jos, Yola da Fatakwal za su samu mafi karancin wutar lantarki saboda 180.90MW, 115.12MW da 213.79MW za su samu.

Yola Electricity Distribution Company Plc (YEDC) ya na samarwa Adamawa, Borno, Taraba da Yobe wuta.

Jos Electricity Distribution Plc (JEDC) ya na samar wa Bauchi, Benue, Gombe da Filato wutar lantarki.

Kamfanin rarrabe wutar lantarki na Port Harcourt DisCo ya na bai wa jihohin Rivers, Akwa Ibom, Cross River da Bayelsa wutar lantarki.

Gwamnatin tarayya ta kara kudin wutan lantarki ba tare da sanar da yan Najeriya ba, Bincike

A wani labari na daban, ba tare da sanin yan Najeriya ba, gwamnatin tarayya ta kara kudin wutan lantarkin da suke amfani da shi a boye ba tare da sanar da kwastomomi ba.

Bincike Jaridar Leadership ya bankado karin da aka yi a Satumba kuma hakan na tabbatar da shirye-shiryen da gwamnatin tarayya ke yi na janye tallafin lantarki.

Kara karanta wannan

Kwastam ta yi babban kamu, ta kame kwantena makare da tramadol na biliyoyi

An aikewa Kakakin hukumar lura da lantarkin Najeriya NERC, Usman Arabi, don ya tabbatar ko karyata wannan labari amma bai amsa ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel