Gwamnatin tarayya ta kara kudin wutan lantarki ba tare da sanar da yan Najeriya ba, Bincike

Gwamnatin tarayya ta kara kudin wutan lantarki ba tare da sanar da yan Najeriya ba, Bincike

  • An bankado yadda aka kara farashin wutan lantarki ba tare da sanin mutane ba
  • Majiya ta bayyana cewa gwamnati tayi hakan ne gudun maganganun da jama'a zasu yi
  • An kara farashin wutan da 2% kuma za'a cigaba da yin karin

Ba tare da sanin yan Najeriya ba, gwamnatin tarayya ta kara kudin wutan lantarkin da suke amfani da shi a boye ba tare da sanar da kwastomomi ba.

Bincike Jaridar Leadership ya bankado karin da aka yi a Satumba kuma hakan na tabbatar da shirye-shiryen da gwamnatin tarayya ke yi na janye tallafin lantarki.

A binciken, majiyoyi daga kamfanonin lantarki sun bayyanawa Jaridar Leadership cewa an ki fadawa jama'a ne saboda gudun abinda ka iya biyowa baya na korafe-korafe.

Kara karanta wannan

Abin da yasa Legas ta zama matattaran mashaya muggan ƙwayoyi, Kakakin Majalisa Obasa

An aikewa Kakakin hukumar lura da lantarkin Najeriya NERC, Usman Arabi, don ya tabbatar ko karyata wannan labari amma bai amsa ba.

Wata majiya ta bayyana cewa karin da akayi na kashi 2% ne kawai kuma bashi da yawa.

Majiyar ta kara da cewa karin ya zama wajibi ne saboda gwamnati ba zata iya cigaba da biyan kudin tallafi ba.

A cewar majiyar:

"Karin ba shi da yawa saboda ba a son mutane su sani, kuma an yi hakan ne da gayya saboda ba'a son abun yayi yawa kan kwastamomi, amma tabbas za'a cigaba da hakan."

Gwamnatin tarayya ta kara kudin wutan lantarki ba tare da sanar da yan Najeriya ba, Bincike
Gwamnatin tarayya ta kara kudin wutan lantarki ba tare da sanar da yan Najeriya ba, Bincike
Asali: UGC

Muna kashe N30bn na tallafin wutan lantarki ga yan Najeriya kowace wata, FG

A bayan Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa kowani wata sai ta kashe akalla bilyan talatin don biyan kudin tallafin wutan lantarkin da yan Najeriya ke amfani da shi.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Gwamnatin Buhari ta ware biliyoyin Nairori ga likitoci, ladan dage yajin aiki

Ta kara da cewa ta rage kudin tallafin da N20bn sabanin N50bn a baya saboda cigaban da aka samu wajen amsan kudin wuta da Discos ke yi.

Gwamnati ta bayyana hakan ne a takardar da ta saki kan cigaban da aka samu a bangaren wutan lantarki a Najeriya, rahoton Punch.

Bayani kan halin da sashen lantarki ke ciki a Najeriya yanzu, gwamnatin tace,

"An kara farashin wutan lantarki da kashi 36% daga Satumban 2020. Kuma an samu karin biyan kudi da kashi 60%."

"An rage kudin tallafin da gwamnati ke biya da N20bn a wata. An samu kudi N65bn a Disamba 2020 sabanin N39bn da ake samu a baya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng