UN ga kasashen duniya: Ba Korona ce kadai annobar ba, akwai wata, kowa ya shirya

UN ga kasashen duniya: Ba Korona ce kadai annobar ba, akwai wata, kowa ya shirya

  • An shawarci gwamnatoci a duk fadin duniya da su karfafa hanyoyin ba da agajin gaggawa kan annobar Korona
  • Majalisar Dinkin Duniya ta yi wannan kiran ne a ranar Litinin, 27 ga watan Disamba a yayin bikin ranar rigakafin annoba ta duniya.
  • Kungiyar ta kasa da kasa ta bayyana cewa yayin da duniya ke fama da Korona, ba za ta zama annoba ta karshe da za a fuskanta ba

Shugabancin Majalisar Dinkin Duniya (UN) ya tabbatar da cewa Korona ba ita ce annoba ta karshe da duniya za ta shaida ba a nan gaba.

Da yake magana a ranar shiri tsaf na rigakafin annoba ta duniya, babban sakatare na Majalisar Dinkin Duniya, António Guterres, ya lura cewa har yanzu duniya ba ta koyi darussa na martanin gaggawa ga annoba daga abin da ya faru a Korona ba, in ji jaridar The Guardian.

Kara karanta wannan

Sabuwar dokar Korona: An hana wuraren ibada da gidajen shakatawa a Abuja taro

Guterres a cikin sakon nasa na ranar Litinin, 27 ga Disamba, ya ba da sanarwar cewa ya kamata kasashen duniya su bullo da shirye-shiryen da za su iya magance lamura cikin gaggawa.

Annobar Korona na nan tafe
UN ga duniya baki daya: Ba a komai ba daga annobar Korona, kowa ya shirya | Hoto: bbc.com
Asali: UGC

Shugaban na Majalisar Dinkin Duniya, don haka ya yi kira ga gwamnatoci da su karfafa cibiyoyin kiwon lafiya, musamman a matakin kananan hukumomi, in ji The Cable.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa:

"Korona ta nuna yadda saurin kamuwa da cuta zai iya mamaye duniya, kassara tsarin kiwon lafiya zuwa mummuna, da sauya rayuwar yau da kullum ga dukkan bil'adama.
“Har ila yau, ta bayyana rashin koyan darussa na daukar matakan gaggawa na kiwon lafiya na baya-bayan nan kamar SARS, muran influenza, Zika, Ebola, da sauransu. Kuma ta tunatar da mu cewa duniya ta kasance cikin bala'in rashin shiri don dakile barkewar annobar da ke yaduwa a kan iyakoki da kuma yaduwa zuwa annoba ta duniya.

Kara karanta wannan

Kudirin gyaran dokar zaɓe: Gbajabiamila ya karanto wa zauren majalisar tarayya wasiƙar Buhari

"Korona ba zata zama annoba ta karshe da dan adam zai fuskanta ba. Cututtukan sun kasance a sarari kuma hadari ne ga kowace kasa.
“Yayin da muke daukar mataki ga wannan matsalar lafiya, muna bukatar mu shirya don na gaba. Wannan yana nufin habaka saka hannun jari a cikin ingantaccen sa ido, saurin ganowa da sauri da tsare-tsaren daukar matakai a kowace kasa - musamman ma mafi rauni."

An wallafa wani bangare na jawabinsa a shafin Facebook na Majalisar Dinkin Duniya.

Rashin da'a ne ke sa likitoci suke tsundumawa yajin aiki, inji ministan Buhari

A wani labarin, ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Chris Ngige, ya ce bai dace likitoci masu tsaron lafiyar al'umma su shiga yajin aikin ba kwata-kwata, Daily Trust ta ruwaito.

Ya yi wannan jawabi ne a babban birnin tarayya Abuja a wajen taron kaddamar da wasu dalibai shida da suka kammala karatun likitanci a Jami’ar Abuja a cikin Majalisar Likitocin lafiya da Hakora ta Najeriya.

Kara karanta wannan

Sanatoci sun shiga ganawar sirri kan sabon kundin zabe 2021 da Buhari ya ki sa hannu

Ya kuma bukaci sabbin daliban da suka kammala karatun likitanci da su gujewa akidar shiga yajin aikin da likitoci ke yi a kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel