Wani mutum ya mutu wurin gasar cin abinci yayin bikin Kirsimeti a Uganda

Wani mutum ya mutu wurin gasar cin abinci yayin bikin Kirsimeti a Uganda

  • Wani mutum mai suna Sentekola Gad ya riga mu gidan gaskiya sakamakon shake makogoronsa da abinci yayin gasar cin abinci
  • An shirya gasar cin abincin ne yayin bukukuwar kirsimeti a Kibimbiri cell, Kabuga, wani yanki na Kanungu a kasar ta Uganda
  • Tuni dai jami'an yan sandan kasar sun bazama neman wadanda suka shirya gasar kan zarginsu da saba ka'idojin shirya gasa irin wannan

Uganda - Wani mutum mai shekaru 56 mai suna Sentekola Gad, ya shake kansa da abinci yayin gasar cin abinci a ranar Kirsimeti a kasar Uganda LIB ta ruwaito.

Mai magana da yawun yan sanda, Fred Enanga, ya ce Sentekola ya shiga gasar cin abinci ne da wani Salvan ya shirya a Kihiri, a yankin Kanungu.

Wani mutum ya mutu yayin gasar cin abincin Kirsimeti a Uganda
Wani mutum ya gamu da ajalinsa wurin gasar cin abinci yayin bikin Kirsimeti. Hoto: LIB
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Bakon lamari: Bidiyon dan sanda na raba wa matafiya buhunan shinkafa ya jawo cece-kuce

A yayin da ya ke yi wa manema labarai jawabi a ranar Litinin, Enanga ya ce:

"Wanda abin ya faru da shi ya shake kansa ne a abinci kuma aka dauke shi aka kai cibiyar lafiya ta Kihihi inda aka tabbatar abincin ne ya kashe shi."

Yan sanda na neman wadanda suka shirya gasar

LIB ta rahoto cewa kakakin yan sandan ya ce jami'an su a halin yanzu suna neman wadanda suka shirya gasar domin ba su bi dokokin tsare lafiyar mutane ba yayin shirya gasar.

Enanga ya ce ya kamata wanda ya hada gasar ya gargadi wadanda za su shiga game da hatsarin da ke tattare da gasar kuma ya kamata ya yi aiki tare da likita.

"A yadda ya kamata, masu shirya irin wannan gasar a kasashen da suka cigaba suna sanar da masu gasar hatsarin da ke tattare da abin sannan su dauki hayar likitoci wanda a wannan ba a yi ba," Enanga ya kara da cewa.

Kara karanta wannan

Minista ya tona asiri, ya ce Jonathan bai bar wa Buhari komai a asusun Najeriya ba

An bude binciken kisa a caji ofis na yan sanda da ke Kabuga mai lamba SD REF 04/26/12/2021.

Kakakin yan sandan ya gargadi mutane game da hatsarin da ke tattare da irin gasa na cin abinci ko shan giya kamar wannan.

Bauchi: Gobara ta lakume babban kasuwar kayan abinci, an yi asarar kayan miliyoyin naira

A wani labarin, mummunar gobara ta afka shaguna cike da kayan abinci makil masu kimar miliyoyi a wani bangare na sananniyar kasuwar kayan abinci ta Muda Lawal da ke jihar, Vanguard ta ruwaito.

An gano yadda wutar ta fara ruruwa da tsakar daren Laraba wacce ta ci gaba da ci har safiyar Alhamis inda ta janyo mummunar asarar kafin jama’a da taimakon ‘yan kwana-kwana su kashe wutar.

Duk da dai ba a gano sababin wutar ba, amma ganau sun ce daga wani shago wanda danyun kayan abinci su ke cikinshi ta fara bayan an kawo wutar lantarki.

Kara karanta wannan

Mu'ujizar Allah ce da kubutar da ni daga hannun yan bindiga, kwamishina ya magantu

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel